Dan takarar Jam'iyyar Memleket Muharrem Ince ya sanar da janyewarsa daga zaben shugaban kasa da za a yi ranar 14 ga watan Mayu / Hoto: AA  / Photo: TRT World

Dan takarar Jam'iyyar Memleket Muharrem Ince ya janye daga takarar shugaban kasar Turkiyya a zaben da za a yi ranar 14 ga watan Mayu, a wata sanarwa ta ban mamaki, inda a yanzu ya rage 'yan takara uku ne kawai ke neman kujerar.

Ince mai shekara 58, ya sha kaye a zaben shugaban kasa na shekarar 2018, wanda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi nasara da kashi 53 cikin 100 na kuri'un. Ince ya samu kashi 30 da doriya cikin 100 ne kawai daga cikin jumullar kuri'un da aka kada.

Ince, wanda ya sanar da janyewar tasa a babban birnin kasar Ankara, bai bayyana dalilinsa na janye wa daga takarar ba.

Sai dai dama can yana fuskantar matsin lamba daga Kawancen Jam'iyyar adawa ta CHP wacce ta zarge shi da raba kuri'un bangaren hamayya sakamakon tsayarwasa takara.

Amma kuma, 'yan takara a karkashin jam'iyyarsa ta Memleket Party za su ci gaba da neman kujerun majalisar dokoki a zaben da ke tafen.

Ince na daga cikin manyan 'yan takarar shugaban kasa hudu da ke fafatawa a neman kujerar, da suka hada da shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan da Kemal Kilicdaroglu da kuma Sinan Ogan a zaben da za a yi ranar Lahadi mai zuwa, 14 ga watan mayun 2023.

TRT World