Ferhat Kopuz, dan kasar Turkiyya da zai bar Istanbul zuwa Sydney, ya jefa kuri’ar farko ta zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki a ranar Alhamis 27 ga Afrilu.
Kopuz ya sauke wannan nauyi nasa na dimukradiyya a sashen jami’an kwastan na filin tashi da saukar jiragen saman Istanbul inda aka ajje akwatunan zabe don ‘yan Turkiyya da za su fita daga kasar ko za su shige ta.
Ga ‘yan Turkiyya da ke rayuwa a kasashen waje, za su gudanar da zabe a tsakanin 27 ga Afrilu da 9 ga Mayu, kamar yadda Hukumar Zabe ta Koli ta sanar. Mazauna cikin kasar kuma za su yi nasu zaben a ranar 14 ga Mayu.
Kusan ‘yan kasar Turkiyya miliyan 3.4 da ke zaune a kasashen waje ne za su iya jefa kuri’unsu a zabukan shugaban kasa da ‘yan majalisar da ke tafe. A zaben da ya gabata an samu kamar miliyan 1.5 da suka yi zabe.
Ofisoshin jakadancin Turkiyya sun samar da cibiyoyin jefa kuri’a a wurare 156 da ke kasashen waje 73.
“Daga yadda abubuwa suke bayyana, mutane sun zaku su jefa kuri’a a wannan karon sama da yadda suka yi a baya. Akwai dogayen layuka a lokacin da masu jefa kuri’ar suke rejistar sunayensu a rumfunan zabe”, in ji Bulent Guven, dan Kasar Turkiyya masanin kimiyyar siyasa kuma mazaunin Jamus da ke rayuwa a Hamburg.
Mafi yawan ‘yan kasar Turkiyya da ke kasashen waje na rayuwa ne a Yammacin Turai, inda ‘yan ci rani suka koma da zama a shekarun 1960 a wani bangare na sake gina duniya bayan Yakin Duniya na II. Su ne baki Musulmai mafiya yawa a Yammacin Turai.
Jamus ce a kan gaba a tsakanin kasashen, wadda ke da masu jefa kuri’a ‘yan Turkiyya miliyan 1.5 inda kuma siyasar Turkiyya za ta yi zafi, sai Faransa da ke biye mata baya, sannan Holan da Beljiyom.
Game da abubuwan da za su ja ra’ayin masu jefa kuri’a kuma, ‘yan Turkiyya da ke kasashen waje na da nasu bukatun da suka sha bam-bam da ‘yan Turkiyya da suke cikin gida.
“Mutane a nan na bayar da muhimmanci ga kimar Turkiyya a kasashen waje, suna alfahari da kasarsu ta samar da motar da ke aiki da lantarki ta Togg, ta samar da jiragen yaki marasa matuka da kuma jirgin yaki na TCG Anadolu, jirgin yakin da aka kaddamar a ‘yan kwanakin nan.”
Idan aka kwatanta da miliyan 61 da za su jefa kuri’a a cikin gida Turkiyya, za a ga kamar kuri’un kasashen wajen ba su da yawa, amma kuma zabinsu na iya yin tasiri kamar yadda aka gani a 2018.
“Ina tunanin adadin masu jefa kuri’a ba zai ragu ba kasa da yadda aka gani a zaben da ya gabata,” in ji Mehmet Kose, tsohon shugaban YTB, Hukumar Kula da Turkawa da Dangoginsu da ke Kasashen Ketare.
Ta yaya ‘yan Turkiyya da ke kasashen waje suke zabe?
A lokacin da aka fara zabuka a kasashen waje a ranar 27 ga Afrilu, Hukumar Zabe ta Koli ta sanya ranaku da lokuta daban-daban don gudanar da zaben a kasashe daban-daban duba da yawan da 'yan Turkiyya ke da shi a kasashen.
A Amsterdam, Holan, a ranar 29 ga Afrilu za a fara jefa kuri’a kuma har zuwa ranar 7 ga Mayu wato kwanaki 9 kenan, in ji Mahmut Burak Ersoy, Babban Jakadan Turkiyya a Amsterdam.
Ya fada wa TRT World cewa “Ranakun jefa kuri’un sun bambanta a kasashe daban-daban, ya danganta da yawan ‘yan Turkiyya da ke rayuwa a kasashen. Sannan za a duba kuma yadda Holland ba wata babbar kasa ba ce kamar Jamus, kuma tafiya zuwa wurare marasa nisa na da sauki.”
Akwai ’yan kasar Turkiyya sama da 280,000 da suke da rejistar zabe a Holan. Kusan dubu 150,000 na zaune a kewayen Amsterdam, amma dubu 40,000 ne kawai ke da rejistar zabe, inji jami’in diplomasiyyar.
Mutane za su iya jefa kuri’arsu daga karfe 9 na safe zuwa 9 na dare a wajen da aka tanada don jefa kuri’ar da ke Babbar Cibiyar Taro ta RAI da ke Amsterdam.
Masu jefa kuri’a za su zo katin dan kasa ko wasu Karin takardu kamar shaidar aure don tabbatar da su waye su.
A wajen jefa kuri’ar, suna bayyana a gaban mambobin zabe biyar, wadanda suke duba idan mutum na da rejista a wannan waje kuma ya cancanci jefa kuri’a.
Mutanen sun kunshi jami’an gwamnatin Turkiyya biyu da wakilai uku daga jam’iyyun siyasa da suka samu mafi yawan kuri’u a zaben da ya gabata.
Wani sabon yayi
Tsawon shekaru, Turkiyya ta kaddamar da gyare-gyaren doka don saukaka wa ‘ya’yanta da ke ketare samun damar jefa kuri’a.
Mislai, ‘yan kasar Turkiyya da ke kasashen waje na cikin jerin masu jefa kuri’a a kundin bayan Hukumar Zabe ta Koli, kuma abun da za su yi kawai shi ne su tabbatar bayanansu sun bayyana kafin a fara zaben, in ji Kose.
Masu zabe za su iya duba bayanansu ta yanar gizo cikin sauki.
Amma a baya abubuwan babu sauki sam.
A shekarun 1950 a takarda ne kawai aka baiwa ‘yan kasar Turkiyya da ke kasashen waje damar jefa kuri’a.
Amma saboda wahalar tafiya zuwa Turkiyya don neman a saka sunan mutum a jerin masu jefa kuri’a ya sanya da yawa suke fasa zuwa zaben, kamar yadda Kose ya yi Karin haske.
A shekarun da suka biyo baya kuma, an saukaka dokokin daga 1987 zuwa sama, ‘yan kasar Turkiyya da ba sa zaune a cikin kasar za su iya jefa kuri’a a kan iyakokin Turkiyya idan za su shiga ko za su fita daga kasar. Duk da haka ba a samu karin yawan masu zaben ba.
“A tsakanin 1987 da 2011, mafi yawan adadin mutanen da suka jefa kuri’a a cibiyoyin kwastan na iyakokin Turkiyya ba su haura 270,000 ba. Adadin dan kadan ne sosai. A wasu lokutan ya ragu zuwa 40,000 ko 50,000,” in ji Kose.
Daga shekarar 2014 ne adadin masu jefa kuri’a da ke kasashen waje ya yi tashin gwauron zabi inda aka kafa akwatuna a garuruwan da ‘yan Turkiyya ke rayuwa.
A 2014, mutane rabin miliyan ne kadai suka jefa kuri’nsu daga cikin miliyan 2.8 da suke da rejista. Shugaba Erdogan ya yi nasara da kaso 62.5 a kuri'un da wadanda ke kasashen waje suka jefa.
Sama da mutane miliyan daya ne suka jefa kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokoki da ya biyo baya a wannan shekarar inda aka kara yawan cibiyoyin zabe a kasashen ketare.
Jam’iyyar AKP ta Erdogan ta sake zama a kan gaba
Bayan kuri’ar raba gardamar da aka gudanar a 2017 da manufar daidaita aiyukan shugaban kasa, adadin masu jefa kuri’a na kasashen waje ya kai miliyan 1.4.
A zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki na 2018 wanda AKP ta yi nasara, ‘yan Turkiyya da ke kasashen waje sama da miliyan uku ne suka jefa kuri’a.
Tun shekarun 1980, ‘yan Turkiyya da ke kasashen waje na zabar masu saukin ra’ayin rikau, hakan ya fara da jam’iyyar Ana Vatan ta Turgut Ozal, in ji Guven, masanin kimiyyar siyasa da ke Hamburg.
‘Wannan ra’ayin rikau ya ci gaba har lokacin da AKP ta kafa gwamnati inda take samun kuri’u daga mazauna kasashen waje.”
Rashin wakilci da 'yan siyasa ‘yan asalin Turkiyya ke samu a siyasar Turai, watakila shi ne dalilin da ya sanya su samun babbar dama a zabukan Turkiyya.
Misali a 1990, akwai ‘yan siyasa ‘yan Holan ‘yan asalin Suriname sama da ‘yan Holan ‘yan asalin Turkiyya. Suriname da take karamar kasa a Kudancin Amurka na da adadin mutane rabin miliyan.
A lokacin Brexit an ga yadda aka nuna kyama ga Turkiyya inda ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau suka kirkiri labarin samun ‘yan Turkiyya da ke kokarin shiga Birtaniya.
Wani dalili da ya sake habaka jefa kuri’ar ‘yan kasar waje shi ne, a karkashin Erdogan, Turkiyya ta dabbaka aiyuka masu tasiri a fannin diplomasiyya a duniya, misali yadda ake dinga fitar da hatsi daga Yukren.