Erdogan (H), shi ne dan takarar Kawancen Al'umma, yayin da babban mai hamayya da shi Kilicdaroglu (D), na jam'iyyar Republican People's Party (CHP) yake takara a karkashin kawancen jam'iyya shida da ake kira Kawancen 'Yan Kasa./ Hoto: TRT World

Za a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Turkiyya na 2023 bayan an rasa samun dan takarar da ya samu fiye da rabin kuri'un da aka kada a zaben ranar 14 ga watan Mayu.

A zaben da aka gudanar ranar Lahadi babu dan takarar da ya samu fiye da kashi 50 na kuri'un da aka jefa, ko da yake Shugaba mai-ci Recep Tayyip Erdogan ne yake "kan gaba".

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce kasar ta kammala wani zagaye na "bikin dimokuradiyya" ranar 14 ga watan Mayu, inda ya kara da cewa zaben na daga cikin wadanda mutane suka fi fitowa a tarihin kasar.

A zagaye na farko ya samu kashi 49.51 na kuri'un da aka kada, a cewar shugaban Hukumar Koli ta zaben kasar (YSK) Ahmet Yener. Babban mai hamayya da Erdogan, Kemal Kilicdaroglu, ya samu kashi 44.88.

Yanzu dai za a fafata ne tsakanin Erdogan da Kilicdaroglu ranar 28 ga watan Mayu.

Kazalika, Sinan Ogan na Kawancen Ata ya samu kashi 5.17, shi kuma Muharrem Ince, wanda ya janye daga takarar a karshen makon jiya bayan an buga takardun jefa kuri'a, ya samu kashi 0.44.

Kashi 88.92 ne na mutanen da ke zaune cikin Turkiyya suka fita zabe. Yayin da kashi 52.69 na masu zabe ’yan kasar Turkiyya suka fita kada kuri'a a kasashen waje, a cewar shugaban Hukumar Koli ta Zaben kasar, Yener.

Ana cigaba da tattara kuri'u 35,874 da aka kada daga masu jefa kuri'a na kasashen waje, in ji shi.

Cikin mutum miliyan 64.1 da suka yi rajistar zabe, kashi 88.92 na masu zaben sun jefa kuri'un a daya daga yanayi na fitowa wurin zabe mafi girma da aka taba gani a kasar tun da ta koma turbar siyasa mai fiye da jam'iyyu biyu a 1946.

Sakamakon zaben ya nuna irin karfin da Turkiyya ta yi wajen tabbatar da mulkin dimokuradiyya, inda 'yan kasar ba sa shayin bayyana ra'ayinsu.

Tsarin zabe

Manyan 'yan takarar biyu sun fuskanci juna ne ranar Lahadi bayan sun kwashe makonni suna yakin neman zabe mai zafi. An samar da akwatunan zabe 192,214 a fadin kasar.

Kowanne mai zabe ya kada kuri'a biyu, daya ta shugaban kasa, daya ta majalisar dokoki, wadanda za su yi wa'adin mulki na shekara biyar.

Fiye da jam'iyyu 30 da 'yan takara indifenda 150 ne suka fafata a zaben.

Akwai manyan kawance da suka shiga zaben kamar haka: Kawancen Al'umma, Kawancen 'Yan Kasa, Kawancen Ata, Kawancen 'Yan Kwadago da kuma Kawancen 'Yan Gurguzu​​​​.

An soma kada kuri'a ne da karfe 8:00 na safe (0500 GMT) inda aka rufe da karfe 5:00 na yamma (1400 GMT) ranar Lahadi.

TRT World