Dokar da aka kafa a shekarar da ta gabata, ta bai wa jam’iyyu damar yin kawance kamar dai yadda a yanzu ake da Kawancen Al’umma da Kawancen Kasa.
Siyasar gudanar da zabe ta Türkiye ta kafu ne tun bayan da aka kafa jumhuriya a 1923.
A yanzu an buga kugen siyasa a kasar sakamakon zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun dokoki da za a gudanar a ranar 14 ga Mayu.
Ba a taba samun yadda jam’iyyun siyasa suka hada kai waje guda suka kafa kawance kamar wannan karon ba.
Kawancen ‘Yan Shida na jam’iyyun adawa, da ya hada da jam’iyyun CHP da IYI sun kulla 'Kawancen Kasa' don kalubalantar 'Kawancen Jama’a' wanda shugaban kasar mai ci Recep Tayyip Erdogan yake jagoranta, da ya kunshi jam’iyyun AKP da MHP da BBP. Tun shekarar 2002 Erdogan yake kan kujerar mulkin Turkiye.
Me kawance kafin zaben yake nufi?
A tsarin dimukradiyya, ba bakon abu ba ne kananan jam’iyyu su hada kai waje guda don tunkarar abokan adawa masu karfi, wanda hakan yake yanzu a Turkiye.
Irin wannan kawance na da salo guda biyu; jam’iyyu za su kara da juna a ranar zabe, sannan su kafa kawance a majalisa, ko kuma za su goyi bayan ‘yan takarar kowanne bangare don samun isassun adadin kujeru.
Har zuwa 2018 dokar zabe ta Turkiye ba ta bayar da dama ga jam’iyyu su hade kai waje guda tare da goyon bayan ‘yan takarar juna da suke zawarcin kujerun majalisa 600 ba.
Amman an sauya wannan yanayi a 2021 bayan gyara dokar zabe mai lamba 7393.
A yanzu jam’iyyu za su iya shiga zabe da siffar kawance su fafata.
Duk da a baya ba a bai wa jam’iyyu damar yin kawancen shiga zabe ba, amma sun dinga hada kai ba a hukumance ba.
Misali, jam’iyyun da suke son yin aiki tare ba za su fitar da dan takara guda daya ba, amma za su umarci magoya bayansu da su zabi dan takarar da ya fito daga daya bangaren da suke ganin shi ne zai iya lashe zaben.
A irin wannan kawance ana raba kujerun majalisar dokoki a tsakanin su.
A 1991 jam’iyyar RP ce ta ke jagoranci kuma Erdogan mambanta ne. RP ta yi kawance da jam’iyyar MCP wadda a yanzu haka MHP ta maye gurbin ta.
Sannan jam’iyyar IDP ‘yar karama ta masu ra’ayin rikau ma ta shiga kawance da RP a wannan lokaci.
Duk da babu wani daga cikin su da ya samu kaso 10 cikin 100 na kuri’un da aka kada, amma sai kawancensu ya taimaka musu wajen samun kaso 17 inda suka tashi da kujeru 62 a majalisar dokoki karkashin inuwar jam’iyyar RP.
Ana yi wa wannan dabara kallon wata babbar nasara ga jam’yyu masu ra’ayin rikau na Türkiye a shekarun 1990.
Tare da kwaskwarima ga dokar a shekarar da ta gabata, a yanzu za su iya hada kai tare da fitar da dan takara daya tilo.
Daya daga cikin sakin layin dokar zaben ya rage kason kuri’u da jam’iyya ta za samu kafin ta samu damar shiga majalisar dokoki.
A zabukan da suka gabata, jam’iyya sai ta samu kaso 10 cikin 100 na kuri’un da aka kada ne sannan za ta iya shiga majalisar dokoki.
A yanzu an rage adadin zuwa kaso 7, wanda hakan zai taimakawa kananan jam’iyyu samun damar shiga majalisar ba tare da samun goyon bayan kawance ba.
A shekarun 1980 ne aka kawo dokar kayyade yawan kuri’un da jam’iyya za ta samu kafin ta iya shiga majalisar dokoki domin rage yawan jam’iyyu kanana a majalisa, wanda hakan ya kan janyo hana ruwa gudu wajen ayyukan dokoki saboda samun yawaitar bambancin ra’ayi.
Jam’iyyar AKP ta Shugaba Erdogan ta samu nasarar kashi 52 na kujerun majalisar dokoki a zaben 2018 tare da hadin gwiwar jam’iyyar MHP.
Kawancen jam’iyyu shida ya fitar da shugaban jam’iyyar CHP Kemal Kilicdaroglu a matsayin dan takararsu na hadin gwiwa. Kilicdaroglu na kan shugabancin jam’iyyar tun 2010.