‘Yan takara hudu ne za su fafata a zaben shugaban kasar Turkiyya

‘Yan takara hudu ne za su fafata a zaben shugaban kasar Turkiyya

Turkiyya za ta za gudanar da zaben Shugaban Kasa da na 'yan majalisar dokoki.
Hukumar Zabe ta Turkiyya na ci gaba da  / Photo: AA

Hukumar Zabe ta Turkyya ta sanar da sunayen wadanda za su fafata da juna a zaben Shugaban Kasar da ‘Yan Majalisar dokoki da za a gudanar a ranar 14 ga Mayu.

Bayanan da aka buga a jaridar gwamnati ta Turkiyya ta bayyana sunayen Recep Tayyip Erdogan da Kemal Kilicdaroglu da Muharrem Ince da kuma Sinan Ogan a matsayin wadanda za su fafata a babban zaben.

Hukumar Zaben ta kuma bai wa ‘yan takara damar gudanar da gangami har nan da jajiberen zabe ranar 13 ga Mayu.

Hukumar Zaben ta sakawa dukkan ‘yan takarar ka’idojin gudanar da gangami da ganawa da masu jefa kuri’a.

Ba za a gudanar da taron siyasa a gine-ginen jami’o’i da gidajen kwanan dalibai ba.

Haka zalika ba za a gudanar da taron siyasa da yin bayanai ba a cibiyoyin jami’an fito da ke iyakokin Turkiyya.

Haka kuma an hana kafa allo ko yin rubutun siyasa a bangwayen gine-ginen gwamnati, wuraren ibada da kan manyan hanyoyi.

AA