Burak Akcapar ya ce Turkiyya za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da yankin Ukraine ya samu 'yancin kai da kuma cin gashin kai a iyakokinta. / Hoto: AA

Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar rikicin da ya girgiza ka'idojin kafa kungiyar sakamakon yakin Ukraine, a cewar mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya.

"Abin mamaki ne a ce ana samun irin wannan al’amari yana faruwa a tarihin wannan kungiya,'' Burak Akcapar ya shaida wa babban taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York a ranar Laraba.

Burak ya bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta kan batun yakin Ukraine, saboda ‘’ƙin amincewar kasa daya da saɓa wa ra’ayin sauran kasashe.

Ya ce "yakin da ke gudana a Ukraine ya haifar da rikicin wakilci a cikin kungiyar."

Turkiyya za ta ci gaba da tsayin daka wajen tabbatar da aminci a yankin Ukraine da 'yancin kai, in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana kan shawarwarin nemo hanyar kawo ƙarshen rikicin.

Turkiyya ta jagoranci duk wani yunƙurin tattaunawar diflomasiyya, kazalika Burak ya jaddada kokarin da kasar ke yi tare da Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin an farfaɗo da shirin samar da hatsi na Tekun Bahar Aswad.

"A yanzu haka muna aiki kafaɗa da kafaɗa da MDD domin farfaɗo da wannan shiri," in ji shi.

"A karshe dai hanyar diflomasiyya muna fatan za ta taimaka mana wajen cimma burinmu na farfaɗo da wannan shiri," in ji Bukar.

Ukraine ta cancanci 'zaman lafiya'

A watan Yuli ne,Rasha ta ki amincewa da tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsi, tana mai ƙorafi kan cewa ƙasashen yammacin duniya ba su cika alkawarin da ya rataya a wuyansu ba, kuma har yanzu akwai takunkumin hana fitar da abinci da taki da aka sanya a kanta.

Musamman dai Moscow ta soki takunkumin da aka ƙaƙaba mata kan tsare-tsare da inshora da kuma biyan kudi.

A bara ne Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya suka ƙulla yarjejeniyar, wacce ta bai wa Ukraine damar jigilar hatsinta ta Tekun Bahar Aswad tare kuma da nasarar rage farashin abinci a duniya.

Kan batun yaƙin Rasha da Ukraine, Akcapar ya ce Ukraine ta cancanci samun "zaman lafiya" wanda zai tabbatar mata da 'yancinta da kuma cin gashin kanta a iyakokinta da ke kewaye da ƙasashen duniya.

Babban jami'in diflomassiyar Turkiyyar ya bayyana cewa ya kamata a hada Ukraine da Rasha a teburin sulhu kan zaman lafiya, yana mai cewa dole ne duniya ta kasance a shirye idan wannan "lokaci da babu makawa ta karaso.''

“Dole ne ‘yan'adam su nemo hanyar da za a bi don daƙile tashe-tashen hankula da kuma magance rikice-rikice cikin lumana, ita ma wannan majalisar dole ne a yi mata gyara,” in ji shi.

"Turkiyya za ta ci gaba da ba da goyon bayanmu ga Ukraine a gaba kuma ba kawai don ta samu nasara a yakin ba, amma don samun zaman lafiyarta," in ji shi.

TRT World