Turkiyya ce kasa ta biyu da ta fi samar da zuma a duniya. Hoto/  Nuran Gunduz

By Nuran Gunduz

Wata rana a watan Yunin 2021, Nuran Eksi, ta zauna a gaban wasu tulunan zuma. Ta zauna a wurin na tsawon sa’o’i – ta nade hannayenta zaune cikin kwanciyar hankali, ta saka abin hannu wanda aka yi da dutsen ruwa, sannan ga nadadden gashinta bisa kafarda.

Jerin tulunan na dauke da kusan kilo 25 na zuma, wadda ta tace. Lokacin ne karo na farko da ta soma debo zuma daga gidan zuma.

A lokacin da annobar korona ta yi kamari, wadda ta jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyaci hali da dokar kulle, da kuma nuna mana cewa za mu iya yada cutar, Eksi mai shekara 53 ta yi ritaya daga aikin da take yi na kamfani.

Eksi na yin shuke-shuke a cikin tukwane. Hoto/ Nuran Gunduz

Ta kafa sabon ‘ofishinta’ a wani wuri da ke kan hanyar birnin Sile a kusa da gabar tekun Baharul Aswad, mai nisa da Istanbul inda ta soma aikinta na ceto duniya.

“Samun ruwan zuma ya wuce debo ta daga sakarta. Lamari ne na yadda nake saka kaina cikin mullahi, inda nake amfani da hannuna domin yunkurin kara gyara duniyarmu,” kamar yadda ta shaida wa TRT World.

Wannan zai matukar taimaka wa yanayin muhallinmu.” Eksi na daga cikin gomman kananan masu kiwon zuwa wadanda suke amfana daga shirin gwamnatin Turkiyya na kokarin samar da zuma da kuma tallafa wa masu kananan sana’o’i.

Tun daga 2006, ana bayar da dama ga masu kiwon zuma su rinka kiwonta cikin dazukan kasar kyauta.

Turkiyya ita ce ta biyu a cikin kasashen da ke samar da zuma a duniya. Ko a bara sai da ta fitar da tan 17,000 na zuma zuwa kasashe 56 wanda ya sa kasar ta samu kusan dala miliyan 46.

Eksi na sane da irin tasirin da kudan zuma ke yi ga muhalli, hoto/ Nuran Gunduz

Soyayyar yanayi

Ba da dadewa ba a watan Yuni da tsakar rana, Eski ta saka rigar kariya fara inda take dan yawo a cikin furannin lavender da rosemary da clover da sage – wadanda duka ta shuka da kanta.

“’Yar wannan gonar na samar da rayuwa ga abubuwa da dama.”

Nuran na shafe kusan sa'o'i 12 a kullum tana kula da zuma. Hoto/  Nuran Gunduz

Kiwon zuma wani abu ne mai wahala. Eksi na yin komai kan fili mai murabba’in mita 2,500 wanda gwamnati ta ba ta.

Tana shafe akalla sa’o’i 12 a duk rana tana kula da zumarta da kuma samun ruwan zuman.

Idan ta gaji, tana shiga cikin dan karamin dakin da ta yi wa kanta da karfe da katako wanda ta yi wa fentin dorawa da ja inda ta rubuta a gaban wurin “idan akwai zuma, akwai rayuwa”.

Tana zaune a kan katifarta ta je ta duba gidan zumarta sa’annan ta dawo ta kurbi shayinta daga wani kofi na katako.

Ta samar da dan dakin da take hutawa a wurin da take kiwon zumar. Hoto/ Nuran Gunduz

Kiwon zuma ya zame mata wani abu mai wahala ganin cea ta saba aikin ofis. Sai dai Eksi ta kasance mace mai son rayuwa a waje.

Duk sa’ar da ta samu lokaci, takan bugi hanya cikin motarta kirar jeep ta tafi gefen gari – abin da ya sa ta san yanayin rayuwa yadda ya kamata.

Gonar zumarta ta habaka a cikin shekaru biyu da suka gabata inda a halin yanzu take kula da kusan zuma miliyan 2.7.

Ko a bara sai da ta sayar da kilo 80 na zuma. “Ina sane da duk wasu furanni da tsirrai da ke kusa da mu. Na daina tsinkar fure daga jikin wata bishiya ko da kuwa ina so saboda na san wasu kudan zuma za su iya shan ruwanta,”

Eksi na matukar son rayuwa a waje. Hoto/ Nuran Gunduz

Zugar kudan zuma suna shiga da fita daga cikin wani akwatin katako da aka huda a gonar Eksi. Tana amfani da hayaki domin kwantar da hankalin kudan a daya daga cikin akwatunan kafin cire marfin da kuma ciro sakar da zumar ta yi a cikin akwatunan.

“Ina mamaki a kullum a duk lokacin da na kalli lamarin. Wata al’umma ce shiryayya ta dubban gudajen zuma wadanda suke aiki kan abu daya. Akwai ma’aikata wadanda suke samar da ruwan zuma, da sarauniyar da ke yin kwai da kuma daruruwan mazan zuma da ke saduwa da ita.”

Tana amfani da hayaki wurin kwantar da hankalin kudan zumar. Hoto/  Nuran Gunduz 

Masu tafiye-tafiye

A Turkiyya, kiwon zuma wani abu ne na gado, inda ake gadar shi iyaye da kakanni.

Kasar wadda ita ce ta biyu wurin samar da zuma bayan China, na sayar da zumar ta ga kwastamomi da ke Amurka da Sifaniya da Jamus da sauran kasashe.

Idan watan Yuni ya zo, masu kiwon zuma daga sauran larduna na zuwa Sile domin kafa gidajen zumarsu a tsakanin itace, wanda hakan ke taimakawa wurin samar da zuma ta musamman wadda ake amfani da ita wurin magance cutar numfashi.

Eksi ta kulla wata kyakkyawar alaka da kudan zuma. Hoto/ Nuran Gunduz

Shugaban kungiyar masu kiwon zuma ta Sile Ahmet Can, ya shaida wa TRT World cewa akwai iyalai 300 da ke rayuwa sakamakon kiwon zuma a Sile haka kuma suna kula da sama da kudan zuma 10,000.

Zumar Sile, wadda ta yi fice saboda dandanonta da launinta, na daga cikin irin zumar da ake samarwa a yankin Anatolia na Turkiyya mai yanayi iri daban-daban.

Kudan zuma daya zai iya samar da kashi 1 bisa 12 na karamin cokalin shayi a tsawon rayuwarsa. Hoto/ Nuran Gunduz

Zumar wadda akasari ake shan ta domin karin kumallo, na daya daga cikin abubuwan da ake amfani da su a kusan kowane gida a Turkiyya.

Idan aka soma samun sauyin yanayi a watan Yuli, masu kiwon zuma kamar irin su Eksi na tara akwatunan zumarsu a cikin babbar mota inda ake kai su arewa maso yammacin lardin Tekirdag sakamakon an fi samun hasken rana a can.

Irin wannan hijirar na taimaka wa kudan zumar daukar fure domin kai wa sauran bishiyoyi da kuma kare sauran furannin daga mutuwa.

“Sun fi samun kwanciyar hankali da kuma samar da ruwan zuma a cikin rana kawai.” In ji Eksi.

Tafiyar da ake yi da zumar a duk shekara na sa kudan zumar na haduwa da furanni irin daban-daban inda kuma suke iya cin abinci daga furannin da dama kuma masu zaki - wannan na bayar da dama ga Eski da sauran masu kiwon zuma su samu zuma mai kyau kuma samfari daban wadda kamshinta ya sha bam-bam.

Eksi ta sayar da kilo 800 na zuma a bara. Hoto/ Nuran Gunduz

Sai dai masu kiwon zumar sun damu a halin yanzu. Yanayin zafi ko sanyi na tasiri ga kudan zuma haka kuma Eksi ta bayyana cewa matsalar sauyin yanayi za ta iya rinka kawo matsala ga samar da ruwan zuman a halin yanzu.

“Akwati guda na sakar zuma a gonata zai iya samar da kilo 30 na zuma. Amma a halin yanzu ya ragu zuwa bakwai ko takwas sakamakon sauyin yanayi,” in ji ta.

Akwati guda na sakar zuma a gonata zai iya samar da kilo 30 na zuma, in ji Eksi. Hoto/ Nuran Gunduz

Masu alkinta muhalli

Wata hujja da ake yawan kyalewa kan batun kudan zuma ita ce wadannan ‘yan kananan halittun na taimakawa wurin samar da abinci.

Sama da kashi biyu bisa uku na muhimman tsirrai zuma ce ke musu dashen kwayoyi. Kudan zuma na shan sama da kashi biyu cikin uku na tsirrai ko ganyen bishiyoyi duniya domin taimaka musu yin ‘ya’ya a yawon da suke yi na nemo abincin da za su ci, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Duk abinci daya bisa uku da muke ci ya dogara ne kansu.

Kudan zuma na matukar bayar da gudunmawa ga rayuwar tsirrai. Hoto/ Nuran Gunduz

Eksi ta yi matukar damuwa kan irin tasirin da kudajen zumarta ke da shi kan yanayin muhalli inda ta ce wannan ne ma ya kara ba ta kwarin gwiwar soma kiwon zuma.

Baya ga taimakawa wurin samar da abinci, kudan zuma da sauran kwarin duniya na taimakawa wurin samar da ‘ya’ya ga tsirrai inda suke da hannu wurin tattalin sama da kashi 90 cikin 100 na bishiyoyin daji a duniya.

Sai dai sauyin yanayi wanda ke jawo tsananin ruwan sama da ambaliyar ruwa da wutar daji da kuma kara amfani da magungunan kashe kwari na matukar kawo cikas ga zuma, kamar yadda wani masani ya bayyana.

Eksi na wayar da kai kan muhimmancin zuma ga muhalli. Hoto/ Nuran Gunduz 

“Zuma na taka muhimmiyar rawa wurin gina muhalli sakamakon suna taimakawa wurin habakar itatuwa da furanni da sauran bishiyoyi, wadanda suke zama babbar hanyar samar da abinci da muhalli ga sauran dubban dabbobi,” in ji Dakta Becca Farnum,” wata masaniyar muhalli ta Jami’ar Syracuse da ke New York.

“Haka kuma sun kasance wani rukuni na musamman na samun abinci tun da tsuntsaye da wasu dabbobin na cin kudan zumar a matsayin abinci.”

TRT World