Waiwaye kan nasarorin manyan manufofin harkokin waje na shugaban Turkiyya Erdogan

Waiwaye kan nasarorin manyan manufofin harkokin waje na shugaban Turkiyya Erdogan

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya jagoranci sama wa Turkiyya karfin soji da na siyasa a duniya.
Shugaba Erdogan na habaka Turkiyya a dukkan bangarori/ Hoto: TRT World

Kasar da ke tsakanin Turai da Gabas ta Tsakiya, Turkiyya ta dinga fadi tashi wajen karakaina a duniya da ke ta sauyawa – daga sauyin kawancen kasa da kasa da rikicin dan adam wadanda yake-yaken basasa da ta’addanci da gudun hijira suka janyo.

A shekaru sama da 20 da suka gabata, wannan abu ya sanya Ankara neman dabarun dabbaka manufofin kasashen waje da suka habaka matsayin Turkiyya a fagen kasa da kasa.

A lokacin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya hau mulki a shekarar 2002, mahukuntan Turkiyya sun karbi kasar da ke da tattalin arziki mai rauni.

A tsawon shekaru, samar da manufofin cigaban tattalin arziki ta hanyar gayyatar masu zuba jari na kasashen waje da sayar da kadarorin gwamnati da samar da ayyukan yi ga matasa ya bai wa Turkiyya damar daidaita manufofinta na kasashen waje.

Amma kuma yadda daidaita dangantakarta da makota ta samu cikas saboda yake-yake da rikice-rikice ya zo da kalubale da damarmaki daban-daban.

Daya daga cikin manyan nasarorin ayyukan diflomasiyyar Ankara shi ne wanzuwar ta sosai a Afirka.

Alaka bisa girmama juna

“A shekarar 2008 ne alakar Turkiyya da Afirka ta bunkasa sosai a lokacin da aka amince da Turkiyya a matsayin abokiyar aiki mai muhimmanci a Tarayyar Afirka.

Kasashe ‘yan kadan ne aka bai wa wannan matsayi” in ji Eyrice Tepeciklioglu, malami a cibiyar Nazarin Afirka da ke Jami’ar ASBU ta Ankara.

Shekaru kadan kafin haka a 2005, Shugaba Erdogan lokacin yana Firaminista, ya zama shugaban Turkiyya na farko da ya je yankin Hamadar Saharar Afirka inda ya je Itopiya da Afirka ta Kudu.

Eyrice Tepeciklioglu ya fada wa TRT World cewa “Ina tunanin ana yawan yin biris da yaddda Turkiyya da kasashen Afirka suke da mahanga iri daya game da batutuwan kasa da kasa.

Kiran da Turkiyya take na samar da duniya mai adalci ga kowa ya samu karbuwa a wajen kasashen Afirka, saboda tsawon lokaci suna neman a ba su damar dama wa da su wajen yanke hukunci kan al’amura da yawa a duniya.”

Turkiyya na goyon bayan Afirka da ke da mutum sama da biliyan daya a cikinta, na samun kujerar din-din-din da ta wucin gadi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Bangarorin biyu kuma na son a dama da su sosai wajen ba su wakilci mai tsoka a Hukumomin Kasa da Kasa irin su Bankin Duniyda Majalisar DInkin Duniya da Kungiyar Kasuwanci ta Duniya.

Turkiyya a 2008 ta zama mamba ta wucin gadi a Kwamitin Tsaro na MDD bayan samun goyon bayan kasashen Afirka.

Bayan kokarin Shugaba Erdogan a 2005 na ziyartar kasashen Afirka, Turkiyya ta kara yawan ofisoshin jakadancinta a nahiyar da suke 12 a 2002 zuwa 44 a 2019.

Ana ganin alamu da tasirin Turkiyya a bangaren manufofin kasashen waje a Afirka.

Neman mafita a lokacin yanke kauna

Tun bayan fara yakin Yukren a 2022, shugabannin duniya suka tashi tsaye. An samu karin damuwar tsoron yakin na iya janyo rikicin da zai mamaye duniya tare da illata tattalin arziki.

A yakin da aka dauki shekara guda ana yi, lokaci daya da Rasha da Yukren suka yarda da wani abu guda shi ne na batun jigilar hatsi ta Tekun Bahar Maliya, wanda Shugaba Recep Tayyp Erdogan da Majalisar DInkin Duniya suka jagoranci tabbatarwa.

Yarjejeniyar ta bai wa Yukren damar fitar da miliyoyin tan na hatsi wadanda suke jibge a tasoshin jiragen ruwanta saboda toshe hanyoyi da Rasha ta yi. Bayar da damar fitar da abincin ya sauko da farashinsa a duniya.

A lokaci daban-daban Erdogan ya samu damar shiga tsakanin Rasha da Yukren don kawo karshen rikicin da suke yi.

Ba kamar sauran mambobin kawancen NATO ba, Turkiyya ta guji makancewa wajen kakaba wa Rasha takunkumi, daya daga cikin manyan kawayenta na kasuwanci.

Amma duk da haka, Ankara ta fi tsayawa ga bangaren Yukren inda ta ki amincewa da mamayar yankin Kremiya da Rasha ta yi a 2014.

Turkiyya kuma na hanzarin taimaka wa kawayenta a lokacin da bukatar hakan ta taso.

Batun jiragen yaki marasa matuka

A kudancin Caucausia, a lokacin da aka samu arangama a kan iyaka tsakanin Armeniya da Azabaijan, Turkiyya ta kai jiragen saman ta marasa matuka bayar da tsaro ga Baku.

Jiragen yaki marasa matuka na Turkiyya sun taimaka wa Azabaijan wajen fatattakar sojojin Armeniya daga Karabakh, wanda yanki ne da ake takaddama a kai.

An sayar da jiragen yaki marasa matuka na Bayraktar da kamfanin Baykar na Turkiyya ya samar ga kasashen duniya 28, kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen sanya masana’antar tsaron Turkiyya zama kan gaba a duniya.

A lokaci guda, Shugaba Recep Tayyip Erdogan bai ba wa rikicin yankunansu damar lalalata manufar Ankara ta samar da zaman lafiya ba.

Wannan na bayyane karara a lokacin da Turkiyya da Armeniya suka fara yunkurin sasanta juna a shekarar da ta gabata, inda suka fara da safarar jiragen sama da bude iyakokinsu don zirga-zirga tsakanin juna.

Hade ‘yan uwa waje guda

A karkashin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, Turkiyya ta taka muhimmiyar rawa a Kungiyar Kasashen Turkawa (OTS) wadda ta hada da Azabaijan da Kazakistan da Kirgizistan da Turkiyya da Uzbekistan da kuma Hungary a matsayin mamba ‘yar kallo.

Wannan kungiya ta hukumomi na da manufar habaka hadin kai mai karfi tsakanin kasashen da suke magana da yaren Turkanci tare da yada manufar tattalin arziki iri guda.

Don kalubalantar tasirin rikicin Rasha da Yukren, kasashen OTS sun hade kai tare da samun matsayi da kawancen inganta tsaro a tsakaninsu.

A karshen shekarar da ta gabata aka amince da Jumhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus a matsayin mambar OTS ‘yar kallo, wanda wannan ma wata riba ce ta diflomasiyya da Ankara ta samu.

Tun shekarun 1970, Tsibirin Cyprus ya rabu gida biyu zuwa na bangaren Turkiyya da bangaren Girka.

Tsaron iyakoki

Yakin basasar da ya dauki sama da shekara 10 a Siriya ya janyo kalubale ga Ankara.

YPG, reshen kungiyar ta’addar PKK a Siriya tsawon shekaru na kai hare-hare a kan iyaka inda suke nufar dakarun Turkiyya da fararen hula.

Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ta’adda ta kasa da kasa.

A lokacin da yakin Siriya ya gajiyar da Damascus wajen kasa tsare iyakokin kasar, ‘yan ta’adda irin su YPG da Daesh sun kara karfi. Gwamnatin Turkiyya ba ta amince da wannan ba.

Tun 2016, Turkiyya ta kaddamar da farmakan soji hudu a arewacin SIriya, duk da manufar korar ‘yan ta’addar YPG. Amma yin hakan ba diflomasiyya kawai yake bukata ba, yana bukatar karin karfi daga cikin Turkiyya.

YPG ta sake sabunta kanta karkashin sunan Mayakan Dimokradiyya na Siriya wanda sun dade suna samun tallafin kudi da makamai daga Amurka.

Duk da cewar Turkiyya wani bangare ce na kawancen NATO da Amurka ke wa jagoranci, amma Amurkan ta yi biris da kiraye-kirayen Turkiyya na ta raba gari da 'yan ta'addar YPG.

A nan ne Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi tirjiya. Yadda Ankara ta hana Finland da Swidin shiga kawancen NATO na nuni da yadda Turkiyya ta tsaya tsayin daka da kafafuwanta don biyan bukatunta.

Kasashen na Nordic suna bai wa ‘yan ta’addar PKK dama da izini su shirya gangami inda suke dinga daga tutocin kungiyar ta’adda a bayyane.

Ayyukan diflomasiyya na Turkiyya don yaki da ‘yan ta’addar PKK da barazanarsu na samun nasara, inda Finland ta dauki matakan magance damuwar Ankara a Bahar Rum.

Amma a tsawon shekaru, Turkiyya ta fuskanci hanin shiga wannan yanki don neman albarkatun mai.

Daidaito ayyukan teku

A shekaru goman da suka gabata, kusan kasashen duniya 12 da suka hada da Girka da Isra’ila suna ta gasar neman albarkatun mai a tekun Bahar Rum. Amma a tsawon shekaru an hana Turkiyya neman mai a wannan yankin da take da iyaka da shi.

Wannan abu ne mara dadi saboda yadda Turkiyya ke daya daga cikin kasashen da suka fi tsayin iyakar teku da Tekun Bahar Rum.

An ki a saka Turkiyya a yarjeniyoyin da ake ta kullawa na ayyukan teku a wannan yanki duk da yadda take da karfi, har ma da yarjeniyoyin da ake kulla wa da Girka da Kudancin Cyprus bangaren Girka, inda suke kebe yankin da suke kira nasu ne suke neman albarkatun mai a cikin sa.

Haka kuma, Girka ta kafa wani yanki na ayyukan kasuwanci nata ita kadai a tsibiranta da dama a tekun Aegean. Wannan yanki na da tsawon mil 200 daga cikin tekun gabar kasar.

Wannan ya bar Turkiyya da iyaka ‘yar karama a teku, kusan ba ta da komai a gabashin Bahar Rum wanda hakan ya sanya Ankara nuna rashin amincewa.

Domin tsare hakkokinta, a 2019 Turkiyya ta sanya hannu kan yarjejeniya da gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita da ke Tarabulus.

Yarjejeniyar ta bayar da dama a shair’ance don neman albarkatun mai a Bahar Rum tsakanin Turkiyya da Libiya.

TRT World