Erdogan ta ƙaddamar da littafi mai ɗauke da nau'ukan girke-girkan Afirka. / Hoto: AA

Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta jaddada yadda abinci yake da tasiri wajen hada kai a yayin wani taron al'adu da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka, inda aka gudanar da bukukuwan abinci da al'adun Afirka tare da matan shugabannin kasashen duniya da wakilan kungiyoyin kasa da kasa.

Bayan taron da aka yi a Gidan Turkiyya (Türkevi) da ke birnin New York a ranar Talata, UWargidan Erdogan ta wallafa jin dadinta a shafin X na karbar bakuncin taron mai taken "Flavours of Africa: Bajekolin Al'adu, Abinci, da Abokantaka," inda kuma aka yi bikin kaddamar da littafin girkinta na nau'ukan abincin Afirka.

"Kamar yadda yake a Turkiyya da al'adu daban-daban a duniya, teburi a Afirka yana hada bambance-bambance da jituwa da kuma zukata tare da kauna," in ji Uwargidan Erdogan, tana mai lura da kyawawan nau'ukan abinci na nahiyar Afirka.

"Don gabatar da wannan taska ga abin tunawa da ɗan'adam, mun shirya littafin, Al'adun Abinci na Afirka," in ji ta.

"Littafin ya ƙunshi girke-girke na gargajiya, tare da kwarewar ɗan'adam a bayansu," in ji ta, tana fatan zai taimaka wajen kiyaye abokantaka. Za a ƙarfafa hakan ne ta hanyar bude gidan al'adun Afirka a Ankara babban birnin kasar Turkiyya, domin bunkasa al'adun Afirka.

Matan shugabannin kasashe da suka halarci taron bajekolin abincin Afirka a New York.

Uwargidan Erdogan ta gana da 'yar Malcolm X

A ranar Talata kuma, uwargidan shugaban kasar ta gana da Ilyasah Shabazz, diyar fitaccen mai kare hakkin jama'a na Amurka Malcolm X, a Gidan Turkiyya.

Erdogan ya bayyana tasirin gwagwarmayar Malcolm X ta neman 'yanci da daidaito da adalci a duniya, da kuma rawar da ya taka a yunkurin yaki da rashin adalci a duk duniya, a cewar wata sanarwa ta hukuma.

Kazalika, sun tattauna irin kamanceceniya tsakanin fadan Malcolm X da kokarin kare hakkin dan'adam da adalci na 'yar fafutukar Turkiyya Sule Yuksel Senler. Sun yi la'akari da yuwuwar ayyukan haɗin gwiwa tare da tushe da aka kafa don adana tarihin fafutukar Senler.

Senler, daya daga cikin fitattun sunaye a gwagwarmayar neman ‘yancin addinin mata Musulmai, ta rasu ne a shekarar 2019. An kafa wata gidauniya mai sunanta bayan shekara guda don karrama ta.

TRT World