Wata ungulu mai suna Mida, wadda aka makala wa 'yar karamar na’ura mai tura bayanai a lardin Eskisehir na Turkiyya, ta dawo daidai wurin da ta tashi bayan ta yi tafiyar kilomita 32,000 da kuma zagaye kasashe tara cikin shekara guda.
Tun farko an kama ungulun ne yayin wani aiki na alkinta ungulu wanda ofishin karamar hukuma mai kula da gandun dabbobi na Eskisehir ya yi tare da hadin gwiwar kungiyar KuzeyDoga.
Midas, ungulu ce ‘yar asalin Masar, wadda aka ayyana a matsayin nau’in tsuntsayen da ke neman gushewa daga doron kasa.
An saki tsuntsuwar ranar 23 ga watan Afrilu domin ta shiga duniya kamar kowane tsuntsu bayan an makala mata ‘yar karamar na’ura.
Ungulun ta shafe kusan watanni biyar a kusa da Eskisehir kafin ta soma hijira zuwa kudu a watan Satumba a daidai lokacin da yanayin wurin ya soma sanyi.
Midas ta wuce ta Iskenderun a ranar 17 ga watan Satumbar 2022 sai ta bulla Syria da Jordan da Isra’ila da kuma Masar.
A lokacin da take kan hanyarta ta zuwa Masar, ta wuce ta mashigin ruwan Suez inda ta shiga Libya sannan ta ketara zuwa Chadi cikin kwanaki biyar.
Bayan ta shiga Chadi a ranar 26 ga watan Satumba, a nan ta yi ta kiwo har zuwa 3 ga watan Nuwamba sai kuma ta tafi Sudan.
Bayan tafiyar da ta yi ta kwana bakwai, Midas ta yi zamanta a Kadugli, babban birnin Jihar Kudancin Kordofan inda ta yi ta shawagi ta garuruwan da ke yankin.
Ta yi zaman watanni biyar da rabi, daga nan Midas ta kama hanyarta domin komawa gida.
A lokacin da Midas ta tsallaka saharar Jordan da Masar ta kai mashigin ruwan Suez, sai ta sake komawa ta asalin hanyar da ta bi inda ta wuce ta kusan duka wuraren da ta biyo a baya ta shige Turkiyya daga Iskenderum a ranar 3 ga watan Afrilun bana.
Ungulu Midas, wadda ta zo Turkiyya domin bazara, ta kammala tafiyar da ta yi ta hanyar zama a Eskisehir, wurin da aka saka mata na’ura bayan tafiyar kwanaki uku.
A lokacin wannan tafiyar, Midas ta tashi sama tashin da ya kai nisan mita 7,436 daga doron kasa a lokacin da take tafiya tsakanin lardunan Mersin da Adana.
Gudun da Midas ta yi mafi yawa a lokacin tafiyar shi ne kilomita 126 a duk sa’a.
Ta yi tafiyar da babu tsayawa mafi tsawo a tafiyar da ta yi a tsakanin Turkiyya da Syria wato tafiyar kilomita 117.