"Wannan waje zai zama wajen samar da manmu na teku, " a cewar Ministan Makamashi Alparslan Bayraktar. / Photo: AA

Turkiyya ta yi maraba da wajen samar da iskar gas ɗinta ta farko na cikin ruwa a yammacin yankin Canakkale.

“Wannan waje zai nunka abin da muke samarwa a yanzu a wajen Haƙar Gas ɗinmu na Sakarya da ke cikin Bahar Maliya. Zai ƙara yawan abin da muke samarwa na cubic mita miliyan 10 (a kowace rana) a zango na farko, zuwa kyubik mita miliyan 20, kuma za mu iya cim ma buƙatarmu ta samun ƙarin gas ga gidaje miliyan 4.4 daga wannan waje kaɗai,” kamar yadda Ministan Makamashin ƙasar Alparslan Bayraktar ya bayyana ranar Juma’a

Ministan ya ƙara da cewa “Wannan waje zai zama cibiyarmu ta samar da gas a cikin teku. Idan muka ƙaddamar da wannan cibiya ta samar da gas, za mu kai muna samar da kyubik mita miliyan 20 nan da shekara daya da rabi, muna fata a 2026, tare da samar da ƙarin kyubik mita miliyan 10. Wannan zai kai mu zuwa matsayin muna samar da 15% na buƙatar ƙasarmu, inda a yanzu muke iya samar da 7.5-8%. Don haka, tabbas wannan muhimmiyar rana ce kuma mai tarihi a gare mu.”

Bayraktar ya kuma bayyana cewa, za a tura jirgin, wanda ya kai girman filin ƙwallon ƙafa uku zuwa wajen da za a ringa aikin haƙar gas ɗin bayan kammala aikin da ya kamata na fara aiki da shi, inda daga nan kuma zai yi aiki na tsawon shekara 20, inda a kullum zai ringa samar gas cubic mita miliyan 10 zuwa 10.5.

Kama hanyar tsayawa da ƙafa wajen samar da makamashi

A cikin 'yan shekarun nan, Turkiyya ta ba da sanarwar gano iskar gas mai yawa a Bahar Maliya, inda aka kiyasta zai kai cubic mita biliyan 710. A halin yanzu, ana samar da 7-8% ne kawai na gas ɗin da ake amfan da shi a cikin gida, wanda ke nuna wani muhimmin mataki na tsayawa da ƙafa a ɓangaren makamashi da rage dogaro da shigo da shi daga ƙasashen waje.

Ƙasar ta kuma ɗauki wasu matakai na tabbatar da makomar makamashinta tare da wasu manyan yarjejeniyoyin kan iskar gas guda biyu a wannan watan, abin da ke ƙarfafa burinta na zama cibiyar makamashin yankin.

TRT World