Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa nasarar yakin Gelibolu kan manyan rundunonin soji a wancan lokacin - wanda ya rayar da jumlar "Ba za a iya wucewa ta Gelibolu ba" - al'amari ne abin girmamawa a tarinin kasar.
"Da suka hadu da masu tsayayen imani, manyan rundunonin sojin duniya sun sha kashi a Gelibolu, inda imani ya yi nasara," in ji shi a wani wako da ya aike na ranar 18 ga Maris ta tunawa da nasarar Yakin Gelibolu da Sojpjin Ruwan Turkiyya suka yi.
Shugaban ya kuma ce wannan gagarumar nasara da aka cimma a Gelibolu - wadda karfin imani da na gwiwar sojoji ya tabbatar, tare da sadaukar jama'a - ta zama ilhamar jajrcewar da ta kai ga Nasarar Kwatar 'Yancin Kai.
"Tare da gwagwarmaya mara misaltuwa a nan, kasar Turkiyya ta zama cibiyar fata nagari ga dukkan wadanda ake zalunta, ta zama ilhama ga kasashe da dama da aka yi wa mulkin mallaka wajen fara yunkurin kwatar 'yancin kai, suna daukar darasi daga Gelibolu sannan kuma daga Yakin Kwatar 'Yancin Kai," in ji shi.
Ya kume ce Gelibolu ba hadin kan Turkawa kawai yake wakilta ba, nasarar na kuma zama a matsayin mai bayyana makomar yankin.
Ya karkare da cewa "Tunawa da cika shekara 109 da Nasarar Yakin Gelibolu, Ranar Shahidan 18 ga Maris', Ina tuna dukkan shahidai da gwarazanmu na wannan rana musamman ma Mustafa Kemal Ataturk. Ina Addu'ar Allah Ya ji kansu, Ya kuma ba su Aljannar Firdausi,"
Yakin Gelibolu: Matsayar Tarihi
An fara Yakin Duniya na I a lokacin da Daular Usmaniyya ta fara yaki tare da kawa Jamus,ins amagoya baya 'yan kasashen waje sama da 30.
Makiyansu, kawancen kasashe a gefe guda, sun hada da sojojin Ingila da Faransa a Australia, Niyu Zelan, India, Nepal da Sanagal.
Yakin Gelibolu a lokacin Yakin Duniya na I , ya zama tarihin yaki da aka fafata aka yi gumurzu a lardin Gelibolu (Canakkale). Dakarun Daular Usmaniyya sun tsare iyakokin Turkiyya tare da hana 'yan mamaya Ingila da Faransa karbe su.
Kawayen sun yi kokarin kwace iko da yankin Gelibolu, daga nan kuma su kutsa su kwace Istanbul, helkwatar Daular Usmaniyya.
Duk da fata da sa rai a farko don samun nasara a saukake, Kawancen kasashen sun sha wahala a ranar 18 ga Maris 1915, a yayin da jiragen ruwan yakinsu suka nutse sakamakon hare-haren bam na dakarun Daular Usmaniyya. Hakan ya sanya Kawancen kasashen shirin fara sabon farmaki a ranar 25 ga Afrlu, wanda ya janyo yaki na tsawon watanni.
Tsaro ta iyakokin kasa
Da yake sa ran dakarun kawancen za su sauka a iyakar Saros Bay, kwamandan runduna ta biyar Liman von Sanders, Janaral dan kasar Jamus, wanda wanda ya taba zama mai bayar da shawara ga Sojojin Daular Usmaniyya a lokacin Yakin Duniya na I, ya bar dakaru a waje dan tsukuku da ke Gelibolu.
A lokacin da sojojin Birtaniya da Faransa suka gaza a farmakin 18 ga Maris, sai suka yi shirin kai dakarunsu iyakar kasa ta Ariburni, Saddulburnu da Kumkale a ranar 25 ga Afrilu don samun damar buda mashigar tekun Gelibolu ta yadda sojojinsu za su iya shigewa su kai farmakai ta kasa.
Farmakan Soji
An fara bangare na biyu na yakin a lokacin da sojojin kawancen kasashen suka sauka a Ariburnu, Saddulburnu da Kumkale.
A farmakinsa na farko, gundumar Alcitepe, Janaral dan Birtaniya Sie Ian Hamilton ya gamu da tirjiya a ranr 25 ga Afrilu. Dakaru daga Australia da Niyuzelan da ake kira Anzac, sun sha kashi sosai a Ariburnu, inda suka isa wajen a wannan rana.
‘Ina umartar ku da ku mutu’
Laftanal Kanal Mustafa Kemal, kwamandan Runduna ta 19, wand adaga baya ya zama wand aya kafa Jumhuriyar Turkiyya, ya aika da runduna ra 57 zuwa ga Ariburni. Rundunar ta mayar da martani ga hare-haren bataliya takwas. Umarnin Mustafa Kemal ga sojojin shi ne "Ina umartar ku da ku kai hari. Ina umartar ku da ku mutu."
A ranar 26 ga Afrilu, a yayin fuskantar mummunan hari daga makiya, ya sake aike wa da runduna ta 72 da kuma Batiran Tsauni na 8 zuwa ga bangaren kudanci. An bayyana ba za a kara tura karin sojoji wajen ba. Kanal Kemal ya ce 'Rana Mafi hatsari ta Fuskantar Makiya".
An yi yakin Kirte na farko a tsakanin 28 da 30ga Afrilu. Kawancen kasashen Birtaniya da Faransa sun gaza kwatar Alcitepe daga hannun Dakarun Daular Usmaniyya.
Sauran dakarun kasashe kawaye sun shiga yakin a karo na biyu a Kirte a tsakanin 6 da 8 a yunkurin kwace Alcitepe, suna neman karin dakaru.
Duk da babbar asarar, Firaministan Birtaniya Winston Churchill ya bayar da umarnin a ci gaba da yakin.
Murabus din Churchill
A ranar 17 ga Mayu, gwamnatin Birtaniya ta bukaci Rasha da ta tura dakarunta zuwa Gelibolu.
Esat Pasha, wanda aka nada kwmandan Rukunin Arewa, ya bayar da umarnin a kai hari Ariburnu a ranar 18 ga Mayu, amma tawagogi hudu na mayakan Daular Usmaniyya ba su yi nasara ba.
An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Daular Usmaniyya da mayaka 'yan mamaya a ranar 23 ga Mayu. tsagaita wutar - don dukkan bangarori su dauki gawarwaki da wdanda aka jikkata - ta fara aiki tsakanin karfe 0930 da 1630. Bayan karfe hudu na yamma dukkan mayaka za su koma sansanonins, sannan za a ci gaba da fafatawa.
An daga likkafar Mustafa Kemal zuwa Kanal
Laftanal Kanal kemal ya samu nasarori sosai a Gelibolu. ya dakatar da matawar mayaka Anzac, wadanda suka sauka a Ariburnu, zuwa ya yankin Chunuk. Daga nan kuma, Sanders ya kara wa Kemal girma zuwa Kanal a ranar 1 ga Yuni.
Sanin cewa za a samu asara mai yawa, Janaral Hamilton ya yanke shawarar kai hari kan Yassitepe-Alcitepe a ranar 19 ga Mayu, a yayin da Daular Usmaniyya ta mayar da martani ga harin.
A Farkon Yakin Kerevizderesi, sojojin Faransa sun kai hari don mamaye yankin, amma ya zuwa 21 da 22 ga Yuni, mayakan Usmaniyya sun fatattake su.
Kasashen kawance, wadand asuka yi yunkurin kwace iko da Zigindere, sun kuma yi rashin nasara a Yakin Zigindere, wanda aka fafata daga 28 ga Yuni zuwa 5 ga Yuli.
Sauka a Suvla Bay
A yayin da kasashen kawance suka yi rashin nasara wajen sauka a ranar 25 ga Afrilu, sai suka fara kai sabon hari a Suvla Bay a ranar 6 ga Agusta.
A karkashin kwamanda Kanal Kemal, dakarun Daular usmaniyya sun yi nasara kan Anzac da dakarun India, inda aka cimma yarjeje niyar bayonet.
Karshen yakin
Gwamnatin Birtaniya ta yanke shawarar janye wasu daga dakarunta daga Gelibolu a ranar 9 ga DIsamba. An kwashe mayaka gaba daya daga Suvla Bay da Ariburnu, amma an bar 'yan sojoji kadan a Saddulbahir har zuwa 20 ga Disamba.
Mayakan Kasashen kawance sun bar Saddulbahir, waje na karshe da suka mamaye a ranar 9 ga Najairu. Bayan sun janye gaba daya Gelibolu, an ayyana nasarar kasar Turkiyya.
Ranar 18 ga Matris daya daga cikin ranakun Nasara ce a tarihin Turkiyya kuma Turkawa na bikin wannan rana don karrama sojojin da suka yi Shahada.
Nasarar 1915 ta baiwa kasar karfin gwiwa sosai wajen shirya fafata yakin kwatar 'yancin kai, wanda a 1923 aka ayyana Jumhuriya bayan rusa Daular Usmaniyya.