A shekarar 2013, Turkiyya ta zamo cikin kasashe na farko da suka ayyana Daesh a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. . / Photo: AA Archive

'Yan sandan Turkiyya sun kama wasu 'yan kasashen waje 22 masu alaka da kungiyar ta'addanci ta Daesh a yayin wani samame a Ankara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya rawaito yana ambato majiyoyin tsaro.

An kama wadanda ake zargin ne kan alakarsu da kungiyar ta'addancin, a cewar wasu majiyoyi da suka nemi a sakaya sunayensu saboda hana su magana da kafafen watsa labarai da aka yi a ranar Litinin.

An kai samamen 'yan sandan ne bisa zargin cewa wadanda ake zargin suna da alaka da 'yan kungiyar Daesh a yankunan da ake rikici kuma sun aiwatar da wasu ayyuka na kungiyar a shekarun da suka wuce.

Sannan kuma 'yan sanda suna neman sauran wadanda ake zargin da aka yi amannar cewa sun tsere tun a lokacin da aka fara samamen a fadin Ankara, kamar yadda majiyoyin suka kara da cewa.

A shekarar 2013, Turkiyya ta zamo cikin kasashe na farko da suka ayyana Daesh a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Kungiyar ta'addancin ta sha kai hare-hare kasar, inda aka kashe fiye da mutum 300 tare da jikkata daruruwa a hare-haren kunar bakin wake a kalla 10, da harin bam bakwai da kuma harin mayakan sa kai hudu.

A martaninta, Turkiyya ta kaddamar da ayyukan ta'addanci a cikin gida da kasashen waje don dakile ci gaba d akai hare-hare.

AA