Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ƙasarsa ta taimaka wajen dakile matsalar ƙarancin abinci a duniya tare da yarjejeniyar hatsi da ta ba da damar fitar da hatsin Ukraine zuwa kasuwannin duniya ta Tekun Bahar Aswad.
“Tare da shirin Bahar Aswad (hatsi) da aka kaddamar tare da Majalisar Dinkin Duniya, mun kare hadarin matsalar yunwa a duniya ta hanyar tabbatar da cewa an tura tan miliyan 33 na kayayyakin hatsi zuwa kasuwannin duniya.
''Za mu ci gaba da ƙoƙarin da muke yi wajen rage nauyin da ke kan yankunan da ke fuskantar barazanar yunwa, musamman nahiyar Afirka," in ji Erdogan a wani saƙon bidiyo na jawabinsa ga taron Ranar Abinci ta Duniya ta 2023 a ranar Litinin.
Turkiyya ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe ''masu karamci'' a duniya ta fuskar taimakon raya kasa, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ɗaukar nauyin gano bakin zaren warware duk wata matsala da ta haɗa da matsalar abinci da ruwan sha, a cewar Erdogan.
Ranar 16 ga watan Oktoba rana ce da duniya ke bikin tuni da ranar da aka kafa Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar (FAO) a shekara ta 1945.
Taken bikin na wannan shekara shi ne ''Ruwa shi ne Rayuwa, Ruwa shi ne Abinci. Ka da a bar Kowa A Baya.''
"Ba mu ga wani bambanci ba tsakanin alkinta yankunan ruwanmu da kuma kare ƙasarmu ba, don haka a matsayinmu na gwamnati mun aiwatar da wasu muhimman ayyuka da za su tabbatar da samar da ruwan sha da abinci a ƙasarmu cikin shekaru 21 da suka gabata," a cewar Erdogan.
Erdogan ya ce, sannu a hankali ɗan'adam na matsawa kusa da tsarin "kawar da yunwa a 2030", batun mafi mahimmancin a cikin ayyukan ci gaba mai ɗorewa da MDD ya sa a gaba.
A cewar hukumar abinci da noma FAO, daya daga cikin mutane tara a duniya na fama da yunwa, in ji shugaban na Turkiyya, yana mai kari da cewa “duk da samar da tan biliyan 4 zuwa 5 na abinci da ake yi a duk shekara a fadin duniya.
"Duk da ƙididdiga ta nuna adadin abincin zai wadatar da yawan al’ummar duniya da aka ƙiyasta zuwa shekarar 2050, abin takaicin shi ne a yau adadin nan bai kai ga isasshen yawan al’ummar duniya ba.
"Domin ton 21 daga cikin tan 127 na abincin da ake samarwa a duk dakika daya a duniya ana asararsa."
A ɗaya ɓangaren kuma, ya ce almubazzaranci da abinci na haifar da saurin kafewar albarkatun ruwa.
Erdogan ya kuma gayyaci dukkan abokan aikinsa da su ƙara himma wajen cimma manufar “kawar da asarar abinci,” da ke zama daya daga cikin shirye-shiryen da uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta ƙaddamar, wanda kuma a yanzu ya zama wani yunƙuri da duniya ta sa a gaba ƙarƙashin inuwar MDD.
"Mu fara daga yau 16 ga Oktoba, Ranar Abinci ta Duniya, ba gobe ba, mu kare abincinmu, mu kawo ƙarshen ɓarnar abinci," in ji Erdogan.