A ranar 17 ga watan Agustan 1999 bayan misalin 3:00 na dare, mummunar girgizar ƙasa ta faru a arewa maso yammacin gundumar Golcuk da ke Kocaeli a Turkiyya.
Girgizar ƙasar mai maki 7.4 ta faɗa a Kocaeli wadda ke ƙasa da tafiyar awa ɗaya zuwa birnin Istanbul, inda aka shafe daƙiƙa 45 ƙasar na girgiza. Wannan girgizar ta sa an samu wasu ƙananan girgizar ƙasar a Ankara da Izmir. Haka kuma illar ta kai ga sauran lardunan Istanbul da Kocaeli da Sakarya da Yalova.
"Har yanzu muna jin raɗaɗin girgizar ƙasar," in ji Bahattin Akyuz, wani mazaunin Yalova wanda a lokacin yake da shekara 14. "An rinƙa ji kamar za a sake samun wata girgizar a daren (a kowace shekara)," kamar yadda Aykuz ya shaida wa TRT.
Tunin da aka yi na wannan girgizar ƙasar a bana ya zo ne tare da wani sabon ciwon jerin girgizar ƙasa biyu da aka samu waɗanda suka faru a yankin Kahramanmaraş na Turkiyya a Fabrairun 2023.
"A daren 16 ga Agusta, muna tunawa da irin raɗaɗin da muka yi fama da shi a kowace shekara," kamar yadda Akyuz ya ƙara da cewa.
Kahramanmaraş na da nisan kilomita 1000 daga Golcuk. Sai dai bala'in biyu da suka faru sun bara irin tabon da aka samu a baya.
Duk da cewa akwai bambanci tsakanin girgizar ƙasar biyu idan aka kwatanta da mutuwar da aka samu, amma tunawa da yadda gidaje suka rushe da tashin hankalin da aka shiga duk iri ɗaya ne.
Turkiyya ta sake ginawa da tunawa
Turkiyya ta yi aiki tuƙuru domin magance ciwonta, da kuma ƙara gina kanta daga bala'in da ta faɗa.
An kafa hukumar Hukumar Agajin Gaggawa da Kiyaye Afkuwar Bala'i ta AFAD bayan girgizar ƙasar da aka yi ta Marmara a 1999. Ayyukansu su ne su ƙara faɗaɗa ayyukan ceto da kula da lafiya da kwantar da hankulan waɗanda bala'i ya afka wa.
Kamar yadda wani bincike da majalisa ta fitar a 2010, ya nuna cewa mutum 17,480 ne suka rasu sannan kusan 45,000 ne suka jikkata sannan kusan mutum miliyan 16 ne wannan girgizar ƙasar ta 1999 ta shafa. Kusan mutum 200,000 suka rasa muhallansu inda gidaje 66,441 da wuraren aiki 10,901 suka rushe.
Gwamnati ta sake gina garuruwan da girgizar ƙasar ta shafa. Bayan bala'in da ya faru na 1999, gwamnati ta gudanar da aikin sake gina Golcuk wanda tuni ya sauya yadda take inda har wasu mazauna ke kiran wurin da "Paris ta Kocaeli".