Ankara ta dakatar da duk wata harka ta kasuwanci da Isra’ila, wanda ya kai na kimanin dala biliyan 9.5 a duk shekara, sakamakon hare-haren da ƙasar ke kaiwa kan Gaza. / Hoto: AA Archive

Ma'aikatar Makamashi da Alabarkatu ta Turkiyya ta yi watsi da wasu zarge-zarge marasa tushe da ke cewa ana jigilar man fetur daga tashar ruwanta ta Ceyhan zuwa Isra'ila.

A wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa "babu jigilar da ake yi ga Isra'ila ko kuma da sunan za a kai kaya Isra'ila."

Kamfanin BOTAS International ne ke kula da bututan mai na Baku-Tbilisi-Ceyhan a Turkiyya a ƙarƙashin wata yarjejeniyar ƙasa da ƙasa tsakanin Azerbaijan da Georgia.

Kamfanin “ba shi da hurumi ko hannu a saye ko sayar da man,” kamar yadda ma’aikatar ta jaddada.

Kamfanonin da ke jigilar mai ta bututun BTC don fitarwa zuwa kasuwannin duniya daga tashar Haydar Aliyev sun mutunta matakin da Turkiyya ta dauka na kin yin kasuwanci da Isra'ila a baya-bayan nan.

Babu kafa ta samun tsaiko

Ankara ta dakatar da duk wata harka ta kasuwanci da Isra’ila, wanda ya kai na kimanin dala biliyan 9.5 a duk shekara, sakamakon hare-haren da ƙasar ke kaiwa kan Gaza.

Gwamnatin Turkiyya ta dauki matakin hana kamfanoni yin amfani da sunan Falasɗinu domin kai wa Isra’ila kayayyaki.

Kamfanoni za su iya nuna cewa Falasɗinu za su kai kaya amma daga ƙarshe su karkatar da kayan zuwa Isra’ila.

Domin dakatar da wannan lamarin, sai Ankara ta fito da matakai uku na tantancewa.

Na farko shi ne ya zama wajibi ga ma’aikatar tattalin arzikin Falaɗinu ta amince da takardar da ‘yan kasuwa suka bayar kan cewa suna son shigar da kayayyakin Turkiyya cikin ƙasar.

Daga bisani ma’aikatar za ta aika da takardar da ta amince da ita ga ma’aikatar kasuwanci ta Turkiyya.

Bayan haka sai ƙungiyar masu fitar da kayayyaki ta Turkiyya ta tabbatar da takardar.

TRT World