A cikin kwanaki 90 da suka wuce, an kama mutum 2,159 bisa zargin ayyukan satar shigo da baki.

Turkiyya ta "kawar" da jumullar 'yan ta'adda 258 yayin aikace-aikacen yaki da ta'addanci 43,490 a wata uku da suka wuce, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida a ranar Laraba.

Harin ta'addanci 44, galibi daga ciki 37, an yi niyyar kai harin bam ne wadanda aka dakile su a kwana 90 da suka wuce, kamar yadda Ali Yerlikaya ya shaida wa manema labarai.

An kama bakin-haure 75,442 yayin ayyukan sintiri 1,285 da aka yi a wata uku da suka wuce, lokacin da aka mayar da 32,500 kasashensu, in ji Yerlikaya.

An fara aikin mayar da sauran bakin-hauren da suka rage, a cewarsa.

Yerlikaya ya ce a kwana 90 da suka wuce, an kama mutum 2,159 bisa zargin ayyukan satar shigo da baki.

Ya kamata a yaba wa aikin sanya iko kan bakin da ba a saba ganinsu ba, baki 'yan kasashen waje kusan 89,400 da ke zaune a birnin Istanbul kadai, wadanda bizarsu ko kuma izinin zamansu ya kare, sun fice daga kasar a tsawon wata uku, in ji shi.

Dakarun da ke kare iyakokin kasa su ma sun cancanci yabo saboda fiye da mutum 59,000 ne aka dakatar daga shigowa kasar a kwana 90 da suka wuce, a cewarsa.

Mahukunta a Turkiyya suna amfani da kalmar "kawarwa" saboda 'yan ta'addan da ake magana sun mika wuya ne, ko an kashe su, ko kuma an kama su.

TRT World