Turkiyya ta katse hanyoyin amfani da Instagram a ƙasar / Hoto: AA

Hukumar yada labarai da sadarwar fasaha ta ƙasar Turkiyya TKM ta ce ta katse hanyoyin amfani da shafin Instagram.

Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa TRT World cewa an dakatar da ayyukan shafin Instagram ne saboda cire wasu abubuwa da aka wallafa waɗanda ke da alaƙa da Haniyeh a ranar makokinsa na ƙasa, suna masu danganta matakin da ''laifuka da aka tara su.''

A ranar Juma'a ne Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya zargi dandalin sada zumuntar, yana mai cewa ''shafin yana hana mutane yada saƙonnin ta'aziyyarsu game da rasuwar shugaban Hamas (Isma'il Haniyeh) ba tare da la'akari da karya ƙa'ido'ji ba.''

"Wannan tsantsar ƙaƙaba takunkumi ne," in ji Altun a cikin wani saƙon da ya wallafa a ranar Laraba a shafinsa na X bayan an yi wa Haniyeh kisan gilla a Tehran.

"Za mu kare 'yancin fadin albarkacin baki daga wadannan shafuka waɗanda a lokuta da dama suka nuna cewa suna hidima ne ga tsarin rashin adalci a duniya," in ji shi.

Turkiyya dai ta ayyana zaman makoki na ƙasa baki ɗaya saboda kisan gillar da aka yi wa shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, kamar yadda Shugaban Ƙasar Recep Tayyip Erdogan ya sanar.

''Don nuna goyon bayanmu ga al'ummar Falasdinu da 'yan'uwanmu Falasdinawa, za mu yi zaman makoki na kwana ɗaya a gobe Juma'a 2 ga watan Agusta, saboda shahadar babban shugaban harkokin siyasa na Hamas Ismail Haniyeh,'' in ji wata sanarwa da Erdogan ya fitar a ranar Alhamis.

"Ina tunawa da Ismail Haniyeh da duka shahidan Falasdinu a cikin rahama kana ina miƙa ta'aziyyata ga al'ummar Falasdinu a madadin kaina da al'ummata,'' in ji Erdogan.

Isra'ila ta yi wa Haniyeh kisan gilla a ranar Laraba a Tehran babban birnin kasar Iran.

Ya zuwa yanzu Tel Aviv ba ta tabbatar ko musanta alhakinta aikata kisan ba.

TRT World