Jami'an tsaron Turkiyya sun cafke 'yan ta'addar Daesh 32 da suka hada da jagoririnsu, wadanda suke shirin kai hare-hare kan wuraren ibada na majami'u da coci-coci da ofishin jakadancin Iraki da ke Turkiyya.
Hukumar Leken Asirin Turkiyya (MIT) a sanarwar da ta fitar a ranar Juma'ar nan ta bayyana sunayen manyan mambobin Daesh din da Mejbel al Shweihi da aka fi sani da Abu Yakeen al Iraqi, da Mohammad Khallaf Ibrahim, mai lakabin Abu Laith, kuma sun shirya kai hari kan majami'u da coci-coci a Turkiyya.
Haka kuma Ihad Elaani mai lakabin Abdullah al Jumaili na shirin kai hari ofishsin jakadancin Iraki da ke Turkiyya.
A farmakin hadin gwiwa da MIT da 'yan sandan Turkiyya suka kai da duku-dukun asuba a garuruwa tara daban-daban, an kama manyan 'yan ta'addar da kuma karin wasu mambobinsu 29.
A yayin kai farmakan, an kuma gano muhimman ma'ajiyar bayanai mallakin 'yan ta'addar.
A 2013, Turkiyya ta zama daya daga cikin kasashen duniya na farko da suka ayyana kungiyar Daesh a matsayin kungiyar ta'adda.
Kasar ta fuskanci hare-haren 'yan ta'addar Daesh a lokuta daban-daban, tare da kashe sama da mutane 300 da jikkata wasu daruruwa a hare-haren kunar bakin wake akalla 10, harin bam guda bakwai, da na manyan makamai hudu.
A martanin da ta mayar, Turkiyya ta kaddamar da kai farmakai kan 'yan ta'addar a gida da waje.