Dakarun tsaron kan iyaka na Turkiyya sun kama wasu mutum 13 da ake zargin mambobin ƙungiyoyin ta'addanci ne a yayin da sue ƙoƙrin tserewa Girka, kamar yadda hukumomin ƙasar suka bayyana.
Dakarun tsaro sun kama mutanen ne a gundumar Edirne da ke arewa maso yammacin ƙasar da ke kan iyakar ƙasar Girka a ranar Talata, a cewar wata sanarwa daga ofishin gwamnan yankin.
Daga cikin waɗanda aka kama ɗin akwai mutum biyar da ake zargin ƴan ƙungiyar ta'addanci ta PKK ce, sai kuma takwas ƴan Ƙungiyar Ta'addanci ta Fetullah, (FETO).
A cikin sama da shekaru 35 da ta kwashe tana ayyukan ta'addanci a kan Turkiyya, PKK - wadda Turkiyya da Amurka da EU da suka ayyana ta a matsayin ta ƴan ta'adda - ta yi sanadin mutuwar mutum sama da 40,000 da suka hada da mata da yara da jarirai.
'Yan ta'addar FETO da shugabansu Fethullah Gulen ne suka kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016 a Turkiyya, inda aka kashe mutum 252 tare da jikkata wasu 2,734.
Ankara ta kuma zargi ƙungiyar ta'addancin da hannu a yunƙurin juyin mulkin da aka daɗe ana kitsawa na son kifar da gwamnatin ƙasar ta hanyar kutsawa cibiyoyin Turkiyya musamman sojoji da 'yan sanda da kuma ɓangaren shari'a.