Turkiyya ta kai hare-hare kan wuraren ajiye makamai da alburusai na kungiyar 'yan ta'adda ta YPG/PKK inda ta lalata wurare da dama sannan ta "kawar" da mayakanta da yawa a wani bangare na yunkurin murkushe kungiyar da ke da mazauni a arewacin Syria.
"A wani bangare na tsarinmu na kare kai kamar yadda Dokar Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 51 ta bayyana, mun kaddamar da hare-hare ta sama kan 'yan ta'adda a yankunan Tel Rifat, Cizire da Derik," a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta fitar ranar Alhamis.
Hukumar Leken Asiri ta Turkish National Intelligence Organisation [ MIT] ce ta kaddamar da hare-haren.
An kai hare-haren ne a wurare 30, da suka hada da rijiyoyin mai da wuraren ajiye shi, da koguna da gidajen karkashin kasa da sauran wuraren da 'yan ta'adda ke buya. An "kawar da" 'yan ta'adda da dama a yayin samamen, in ji sanarwar.
Ta kara da cewa Rundunar Sojojin Turkiyya za ta ci gaba da yaki da ta'addanci har sai ta kawar da 'yan ta'adda baki daya, tana mai cewa an dauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin hare-haren ba su shafi farar-hula da gine-ginen tarihi da muhalli ba a yankunan da aka kai samamen.
Turkiyya ta kai hare-hare kan 'yan ta'addan ne bayan PKK/YPG ta kai hari a Ma'aikatar Cikin Gida da ke Ankara ranar Lahadin da ta gabata. A harin da ta kai, wani dan kunar-bakin-wake ya tashi bam din da ke jikinsa, yayin da jami'an tsaro suka kashe daya dan ta'addan a kofar shiga ma'aikatar.
Jami'ai a Turkiyya sun ce an kitsa harin ne daga Syria kuma 'yan ta'addan sun fito ne daga arewacin Syria. An jikkata 'yan sanda biyu sakamakon harin.
Hare-haren kungiyar 'yan ta'adda ta PKK
Tun daga 2016, gwamnatin da ke Ankara ta kaddamar da hare-hare da suka yi nasara kan 'yan ta'adda a arewacin Syria da zummar hana su sakat da kuma neman sake tsugunar da mazauna yankin da 'yan ta'adda suka addaba. Ta kaddamar da shirye-sirye uku na kawar da 'yan ta'adda wadanda aka yi wa lakabi da: Euphrates Shield (2016), Olive Branch (2018), da Peace Spring (2019).
Kungiyar PKK ta kwashe fiye da shekara 35 tana kai hare-hare a Turkiyyya — kuma Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai — sun dora mata alhakin kashe fiye da mutum 40,000, ciki har da mata, kananan yara da jarirai. Tana da reshe mai suna YPG a Syria.
A gefe guda, Ministan Tsaron Turkiyya Yasar Guler ya shaida wa Sakataren Tsaron Amurka Lloyd James Austin cewa a shirye Turkiyya take ta shiga yakin da Amurka ke yi da mayakan kungiyar ta'addanci ta Daesh a yankin.
A tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin hada kai don yakar ta'addanci.