Jiragen yaƙin Turkiyya sun ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a kan maɓoyar ƙungiyar PKK a arewacin Iraƙi bisa bin tsarin Majalisar Dinkin Duniya na kare-kai, kamar yadda Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta sanar.
Wasu ƴan ta'adda biyu sun kai harin ta'addanci a Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Turkiyya a babban birnin ƙasar Ankara, a ranar Lahadi da yamma, sa'o'i kaɗan kafin Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya gabatar da jawabi ga majalisar dokoki.
"An kashe 'yan ta'adda da dama ta hanyar amfani da harsasai a samamen da aka kai," a cewar Ma'aikatar Tsaro a wata sanarwa da ta fitar.
A yayin samamen, an kai hare-hare kan wasu maɓoya 20 na ƙungiyar PKK da suka haɗa da cikin kogo da sansanoni a yankunan Metina da Hakurk da Kandil da kuma Gara a arewacin Iraƙi, kamar yadda sanarwar ta fada.
An ƙaddamar da hare-haren saman ne don "daƙile hare-haren ƴan ta'adda a kan mutanenmu da dakarun tsaronmu daga arewacin Iraƙi ta hanyar kawar da PKK/KCK da sauran ɓurɓushin ta'addanci tare da tabbatar da tsaron kan iyakarmu," in ji ma'aikatar.
Harin ta'addanci
A ranar Lahadi da maraice ne wani ɗan ƙunar-baƙin-wake ya dasa bam a kusa da ƙofar shiga Sashen Tsaro na Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, lamarin da ya yi sanadin jikkatar ƴan sanda biyu.
Ma'aikatar tsaron ta ce an kashe ɗaya maharin a musayar wuta da ƴan sanda.
A yanzu haka ƴan sandan biyu da suka ji rauni suna asibiti, kuma ba sa cikin barazanar rasa rayukansu, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya Ali Yerlikaya. Ofishin Atoni Janar na Turkiyya da ke Ankara ya ƙaddamar da bincike kan harin ta'addanci.
Hukumomin Turkiyya sun gano maharin na farko inda suka ce ɗan ƙungiyar PKK ne, sannan ana ci gaba da ƙoƙarin gano ɗan ta'addan na biyu.