Tare da Turksat 6A, Turkiyya ta isa ga sabon fage a fannin kera tauraron dan adam, in ji Erdogan. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa duk da ƙalubale da matsin lamba, Turkiyya na faɗaɗa wanzuwarta a sararin samaniya, yana mai nuni ga sabon tauraron ɗan'adam na TurkSat 6A da ƙasar ta aika sama.

A ranar Litinin da misalin karfe 7:30 na maraice kumbon Falcon 9 na kamfanin SpaceX ya harba tauraron ɗan'adam ɗin mai suna Turksat 6A daga tashar Cape Canaveral Space Force da ke birnin Florida na Amurka zuwa sararin samaniya.

Erdogan ya ce Turkiyya ta kuma aika da tauraronta na Turksat 5B zuwa samaniya shekaru biyu da rabi da suka gabata, yana mai ƙarawa da cewa "Muna jin daɗin yadda muke ƙara ƙarfafa haɗin kanmu da Elon Musk da SpaceX a fannoni daban-daban."

Ya ce Turkiyya ta kammala kashi 81 na ayyukan samar da tauraron Turksat 6A, wanda yake da muhimmanci ga makomar ƙasar a wannan fanni.

A wani ɓangare na ayyukanta a sararin samaniya, Turkiyya ta cim ma burinta na aika ɗan'adam a karon farko zuwa sararin samaniya.

Tare da Turksat 6A, Turkiyya ta buɗe sabon fage a fannin ƙera tauraron ɗan'adam, in ji Erdogan.

Ya kuma ce Turksat 6A zai ƙara ƙarfin tattara bayanan taurarin ɗan'adam na Turkiyya, ciki har da na yankunan India, Thailand, Malaysia da Indonesia.

Tare da samar da Turksat 6A, ayyukan Turksat ga ƙasashen waje za su ƙaru, kuma Turkiyya za ta shiga jerin ƙasashen da suka samar da tauraron ɗan'adam nasu na kansu.

Shugaban na Turkiyya ya kuma ce yana da muhimmanci yadda ƙasar ta iya samar da tauraronta na sadarwa da kanta ba tare da tsoma hannun wata ƙasar waje ba.

'Aikin fasahar ƙere-ƙere mafi kyau'

Turksat 6A, tauraron ɗan'adam na farko da Turkiyya ta samar da kanta "ya kasance aiki mai girma na fasahar ƙere-ƙere da ƙasar ta samar," in ji Mataimakin Shugaban ƙasar Turkiyya Cevdet Yilmaz.

"Turksat 6A, aiki ne na fashar ƙere-ƙere na ƙasarmu da muka ƙaddamar da kyakkyawar niyyar tabbatar da aiki da kuma ilimi da injiniyoyinmu suke da su da ma ƙoƙarin masana'antar kayan tsaronmu," in ji Yilmaz a wajen bikin ƙaddamar da tauraron da aka gudanar a Ankara.

Ya ce "Muna kallon aikin da matuƙar muhimmanci da ganin ya zama 'yantacce a wannan ɓangare da ma fasahar cikin gida."

Yilmaz ya ƙara da cewa matakin samar da tauraron zai bayar da damar fitar da irin ayyukan zuwa ga ƙasashen ƙetare. Kazalika za a iya sayar da kayan aiki da ƙananan tsare-tsare ga ƙasashe da kamfanonin waje, wanda zai ƙara haɓaka kayayyakin da ake fitarwa daga Turkiyya musamman a fannin fasahar ƙere-ƙere.

TRT World