Turkiyya na bikin cika shekaru 101 da zama jamhuriya tare da gudanar da bukukuwan tunawa da wannan gagarumin tarihi da ƙasar ta kafa.
An samo bukukuwan ne a birnin Ankara, inda shugaba Recep Tayyip Erdogan, tare da wasu manyan jami'an gwamnati da na soja, suka kai gaisuwar ban-girma a maƙabartar Anitkabir da aka binne shugaban da ya kafa jamhuriyar wato Mustafa Kemal Ataturk.
Erdogan ya jaddada tsayin daka da kuma jajircewar Turkiyya wajen ɗorawa daga kuɗurin ci gaba na Atakurk ga ƙasar.
A bana dai an faɗaɗa bikin a dukka faɗin kasar, inda aka gudanar da manyan shirye-shirye a Istanbul tare da haskaka gadar Bosphorus da wuta mai ƙyalli.
'Yan ƙasar, tun daga ’yan makaranta zuwa jami’ai, sun taru domin gabatar da fareti da raye-raye da kaɗe-kaɗe, da kuma wasan wuta, suna masu nuna haɗin-kai da alfahari da ƙasarsu.
A ɓangaren ƙasa da ƙasa kuwa, ofisoshin jakadancin Turkiyya su ma sun gudanar da irin waɗannan tarurrukan, yanayin da ya nuna martabar Turkiyya a duniya.
Bikin na bana bai tsaya ga iya murna da kuma girmama tarihin ƙasar ba, har da bayyana irin nasarori da kuma ƙudurin da Turkiyya ta sa a gaba, musamman a fannin ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Erdogan ya miƙa sakon nuna farin ciki da kyawawan ɗabi'u na Jamhuriyar tare da bayyana kuɗurin ƙasar a matsayin jajirtacciya a idon duniya.