Turkiyya da Nijar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da nufin bunƙasa huldar tattalin arziki, musamman a fannin haƙar ma'adinai.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata a yayin wata ganawa da tawagar gwamnatin Nijar da jami’an Turkiyya suka yi a Istanbul.
Ziyarar da jami'an Nijar ta kai Turkiyya a ƙarkashin jagorancin Ministan Ma'adinai na kasar Abarchi Ousmane na daga cikin kokarin da ake na ƙarfafa alaƙa tsakanin kasashen biyu.
''Na yi imanin cewa, sa hannu kan yarjejeniyar za ta samar da ci gaba tare da haɗin gwiwa a fannin hakar ma'adinai," in ji Ministan Makamashi da albarkatun ƙasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar.
"Ina fatan wannan yarjejeniya, wacce za ta taimaka wa ci gaban kasashen biyu, za ta amfanar da kasashenmu dukka," a cewar sakon da Bayraktar ya wallafa a shafinsa na X.
Bayraktar ya jaddada cewa, Turkiyya za ta haɗa kai da Nijar "a kan aikin haƙo ma'adinai da wasu albarkatun ƙasa."
Alaƙa mai cike da tarihi
Ana sa ran dai yarjejeniyar za ta fadada haɗin gwiwa da ke tsakani wajen samar da dauwamamman ci gaba a bangaren hako ma'adinai na ƙasashen biyu da kuma karfafa gwiwar kamfanonin gwamnati da na Turkiyya masu zaman kansu da za su na gudanar da ayyukan hakar ma'adinai a Nijar.
Ziyarar da jami'an na Nijar suka kai na zuwa ne bayan watai uku da irin wannan ziyarar da jami'an Turkiyya suka kai, inda ministan makamashi da albarkatun kasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar ya gana da takwaransa na Nijar a Yamai.
A yayin ganawar da aka yi a watan Yuli, wadda ta samu halartar ministan man fetur na Nijar Mahaman Moustapha Barké da ministan makamashi Amadou Haoua, kasashen biyu sun rattaba hannu kan "Ayyana haɗin gwiwa a fannin mai da iskar gas.”
Turkiyya da Nijar sun jima suna da dangantaka ta tarihi da al’adu tun zamanin Daular Usmaniyya.
A ‘yan shekarun nan ƙasashen biyu sun ƙara mayar da hankali kan yauƙaƙa dangantaka a tsakaninsu.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen yammacin duniya waɗanda suka haɗa da Faransa da ta yi wa Nijar mulkin mallaka da Amurka da kuma Jamus ke ci gaba da shan kaye a yankin Sahel na Afirka, inda ake yi ta samun sauye-sauyen gwamnatoci tun shekara ta 2020.
Akwai ƙasashe da dama a yankin, waɗanda suka haɗa Nijar da Mali da Burkina Faso waɗanda suka yanke alaƙa da Ƙasashen Yamma tare da rungumar sabbin ƙawaye ta a ɓangaren tattalin arziƙi da tsaro inda Turkiyya ke ɗaya daga cikin waɗannan ƙasashen.