Mataimakin Ministan Kasuwanci na Turkiyya ya ce yana da yaƙinin cewa za su cimma burinsu na dala biliyan 10. / Hoto: AA

Turkiyya da ƙasar Girka sun yi cinikayya da ta kai ta dala biliyan 5.8 a 2023, amma a halin yanzu ƙasashen na son cinikayyar ta kai ta dala biliyan 10, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

“Mu makwabta ne, mu abokai ne da Girka. Akwai buƙatar mu yi amfani da wannan lokacin yadda ya dace , akwai buƙatar mu cike giɓin kasuwanci,” in ji Mataimakin Ministan Kasuwanci na Turkiyya Mustafa Tuzcu a ranar Juma’a.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taron kasuwanci na Turkiyya da Girka wanda aka shirya a birnin Santambul.

Tuzcu ya jaddada muhimmancin yarjejeniyoyi 15 waɗanda aka saka wa hannu a ƴan watannin da suka gabata ta ɓangarori da dama inda ya ce yana da yaƙinin cewa za su cimma burinsu na dala biliyan 10.

Firaiministan ƙasar Girka Kyriakos Mitsotakis da Shugaban Turkiyya Erdogan sun saka hannu kan wata yarjejeniyar ƙawance da maƙwabtaka a birnin Athens a ranar 7 ga watan Disamba.

Haɗa kai ta ɓangarori da dama

A ɗaya daga cikin ɓangaren taron, an kuma gudanar da taro karo na shida na Hukumar Haɗin Gwiwar Tattalin Arzikin Turkiyya da Girka.

A lokacin taron, an yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi makamashi da noma da sufuri da masana’antu da noma da yawon buɗe ido da batun kuɗi.

An jaddada cewa, za a samar da ingantacciyar hanyar isar da wutar lantarki mai dorewa a tsakanin kasashen biyu tare da kafa sabon layin sadarwa.

A fannin masana'antu, an amince da bunkasa hadin gwiwa tsakanin kanana da matsakaitan masana'antu na kasashen biyu.

A ɓangaren samar da inganci kuwa, an bayyana cewa, Cibiyar Kula da Inganci ta Turkiyya a shirye take ta hada kai da takwarorinta na Girka.

Har ila yau, an bayyana cewa, bangaren Turkiyya a shirye yake ya ba da bayanai kan masana’antu, kuma an yanke shawarar shirya taron "Zauren yawon bude ido na Girka karo na 10" nan gaba don bunkasa hadin gwiwa a fannin yawon bude ido.

AA