“ “Ba za mu tsaya ba, ba za mu huta ba, har sai mun gina kasar Turkiyya, inda zaman lafiya, kwanciyar hankali, adalci, ci gaba da ‘yan uwantaka ke wanzuwa a kowane wuri na kasarmu." / Hoto: AA

“August Ataturk, muna sake tunawa da irin daukakar da ka yi da alheri a bikin cika shekaru 86 da rasuwar ka," kamar yadda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya rubuta a littafin Anitkabir.

A wani biki da aka gudanar a ranar Lahadi, Erdogan ya bi sahun al'ummar Turkiyya wajen bikin tunawa da wanda ya kafa Jamhuriyar Mustafa Kemal Ataturk a Anitkabir, wurin da aka binne shi ​​da ke kallon Ankara babban birnin kasar.

"Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukakawa da karfafa Jamhuriyar Turkiyya, gadon da ka bar mana da sauran shahidanmu, a kowane fanni, da kara habaka ta cikin tsaro da kwanciyar hankali duk kuwa da rikice-rikicen da ke kusa da ita," kamar yadda Erdogan ya ƙara cewa.

“Ba za mu tsaya ba, ba za mu huta ba, har sai mun gina kasar Turkiyya, inda zaman lafiya, kwanciyar hankali, adalci, ci gaba da ‘yan uwantaka ke wanzuwa a kowane wuri na kasarmu. Allah Ya jikanka" kamar yadda ya rubuta.

Kamar yadda aka saba a wannan al'ada a Turkiyya, a ranar 10 ga Nuwambar kowace shekara ana dakatar da duk wasu abubuwa na rayuwa da misalin 9:05 na safe, inda jiniya ke ƙara a faɗin ƙasar domin alamta daidai lokacin da da Ataturk ya rasu yana da shekara 57, inda miliyoyin mutane a faɗin duniya ke yin shiru na minti biyu.

Sadaukarwa ga ƙasa

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da sauran jami'ai sun tuna da Ataturk.

"Muna ci gaba da riƙe manufofinmu na ƙasashen waje, waɗanda ke wakiltar tsarin 'yancin kai na Turkiyya da kuma matsayar da muke da ita, kuma muna ci gaba da gwagwarmaya irin wadda muka gada daga kakanninmu," kamar yadda Fidan ya bayyana.

Shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus ya wallafa saƙo a shafinsa na X inda ya ce: "A wannan karon, muna jaddada aniyarmu ta kara ciyar da Jamhuriyarmu da kasarmu gaba tare da hadin kan kasa, 'yancin kai, da sadaukar da kai ga 'yancin kan kasa."

A ranar 19 ga watan Mayun shekarar 1919 ne aka fara yakin neman ‘yancin kai na Turkiyya a hukumance. Nasarorin ban mamaki da aka samu a fagen daga sun kai ga samun ‘yancin kai na Turkiyya wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Turkiyya a ranar 29 ga Oktoban 1923.

Al'ummar Turkiyya sun saba ziyartar kabarin Ataturk duk ranar 10 ga watan Nuwamba domin girmama wanda ya kafa kasar.

TRT World