Turkiyya na gudanar da aiyuka a matakin kasa da kasa don tabbatar da tsaro a duniya/ Hoto: TRT World

Gudunmowar Turkiyya ga yankunan gabar Tekun Atlantika na da matukar muhimmanci duba da yadda yankin ya kasance na kasashe mafiya muhimmanci a kawancen NATO, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu.

Ministan ya ce fasalin tsaro na Turai ‘ba ya aiki sam’ a yanayi da lokacin da ya dace.

A lokacin da yake bayani a wajen Babban Taron Tsaro da aka gudanar a Istanbul a ranar Talata, Mevlut Cavusoglu ya ce “A bayyane yake karara tsarin tsaron Turai ba ya aiki yadda ya kamata a lokacin da ya dace, kamar yadda mu Turkiyya muke son gani. Abun takaici wasun su ma ba sa aiki gaba daya.”

Ya lura da cewa “Babu hikima ko dalilin hasashen wani sabon salon tsaro” a lokacin da ake ci gaba da yaki a Yukren.

Cavusoglu ya kara da cewar “Gudunmowar Turkiyya ga yankunan gabar Tekun Atlantika, na da matukar muhimmanci duba da yadda yankin ya kasance na kasashe mafiya muhimmanci a kawancen NATO.”

Babban Taron Tsaro na Istanbul da ake gudanarwa tsakanin 2 da 3 ga Mayu, zai yi duba kan barazanar tsaro a yankuna da ma duniya baki daya, tare da kawo mafita, kamar yadda Ofishin Daraktan Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya ya bayyana.

Ana kuma tsaron babban taron na kasa da kasa zai kunshi masu jawabi kusan 70 daga ciki da wajen Turkiyya da suka hada da ‘yan siyasa da jami’an gudanarwa da malaman jami’a da kwararru da ‘yan jaridu da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa.

Da yake tunatar da cewa kaso 60 na yake-yaken kasa da kasa da ake yi na kewaye da Turkiyya, Cavusoglu ya bayyana cewar tsaro “Batu ne da ya fi karfin a rarrabe shi kan karami da babba, yana bukatar a tunkare shi gaba daya ne.”

Hanyoyi uku na tabbatar da tsaro

A yayin da yake lissafa sharuddan tabbatar da tsaro a yau, Ministan na Harkokin Wajen Turkiyya ya ce daya daga cikin su shi ne “Kasa ta zama mai karfi da jajircewa a dukkan bangarori.”

Ya ce “A lokacin da hukumomin tsaro da jajirtattun al’ummu suka hada kai waje guda tare da hanyoyin jagoranci, sai a samu nasara. Hakan ya sanya mu Turkiyya muka dauki masana’antar tsaro tare da ba ta fifiko.”

Ya ci gaba da cewa Turkiyya a ko yaushe za ta kasance tare da kawayenta, kuma wasu kawaye sun bai wa Turkiyya kunya.”

Cavusoglu ya kuma kara da cewa “Abun kunya ne sosai yadda nake jin a yi kira ga kawaye da kar su saka wa kawayensu takunkumai.”

Ministan na Turkiyya ka kara da cewar hanya ta biyu ta tabbatar da tsaro ita ce “A zama mahanga daya tare da cike gibin juna wajen samar da tsaro ga juna.”

Ya ce “Ta’addanci na daya daga cikin manyan barazanoni da NATO ke fuskanta, kuma dole dukkan kawaye su hada kai waje guda don yaki da wannan annoba.” Ya jaddada cewar “Turkiyya ce kasar da ke yaki da ta’addanci da gaske.”

A yayin kira ga kawayen Turkiyya, ya ce duk kasar da za ta kashe ‘yan kasa da sojojin kasar da take kawance da ita, to ba za a kira ta ingantacciyar kawa ba.

Ministan na Turkiyya ya ci gaba da cewa “Fahimtar tsaro ta mahanga mai fadi da kuma samar da mafita ce hanya ta uku ta warware matsalar tsaro.”

Ya ce “Turkiyya wayayyiya ce, mai kyautayi, karfaffa kuma mai karfin fada a ji da ke amfani da dukkan wani iko da take da shi.”

Ya kuma ce Turkiyya za ta ci gaba da shiga tsakani da taka rawa a matsayin mai rajin ganin an samu tsaro a duniya, ta hanyar ayyukan jin kai da dabbaka manufofin kasashen waje da suke magance matsalolin da ake da su.

TRT World