Kamfanin kera motoci na Turkiyya Togg zai samar da motoci 28,000 kirar jif samfarin T10X zuwa karshen shekarar nan, kamar yadda ministan masana’antu da fasaha ya bayyana.
Kamfanin dillancin labarai na Turkiyya ya ruwaito cewa Fatih Kacir ya kai ziyara kamfanin kera motocin da ke Bursa a ranar Alhamis inda ya ce motocin Togg da ke bisa kwalta a halin yanzu sun zarta 2,000.
Ya bayyana cewa kirar motocin za ta karu da kashi biyu da rabi zuwa shekara mai zuwa.
Mehmet Simsek, wanda shi ne ministan kudi da ajiya na Turkiyya shi ma ya kai ziyara kamfanin kera motocin inda ya ce: "Kera kusan kashi 90 cikin 100 babbar nasara ce. Babban kamfanin fasaha ne wanda yake da manyan fasahohi kuma yana aiki yadda ya kamata.”
Kamfanin Togg wanda aka kafa a 2018, ya soma samar da mota mai amfani da lantarki ta gwaji a Disambar 2019.
Kamfanin ya soma kera motoci gadan-gadan a Oktobar bara.