TCG: Jirgin ruwan yaki mafi girma na Turkiyya da ke iya daukar jiragen sama ya fara aiki

TCG: Jirgin ruwan yaki mafi girma na Turkiyya da ke iya daukar jiragen sama ya fara aiki

Jirgin ruwa TCG Anadolu na da ikon daukar jiragen sama masu saukar ungulu, jiragen yaki marasa matuki da motocin yakin da jiragen yaki marasa nauyi da sojoji.

A ranar Litinin din nan aka mika wa Rundunar Sojin Ruwan Turkiyya jirgin ruwa na TCG Anadolu na yaki kuma mara matuki wanda shi ne irin sa na farko a duniya.

Wannan jirgi da aka kera a Turkiyya zai kara karfafa Rundunar Sojin Ruwan kasar, kuma Turkiyya ta zama daya daga cikin kasashe tsiraru da suka samar da irin wannan jirgi da kansu.

Jirgin ruwan da aka kera a masana’antar jiragen ruwa ta Sede da ke Istanbul, an ba shi sunan TCG Anadolu, kuma yana iya daukar jiragen sama masu saukar ungulu da jiragen yaki marasa matuki da motocin yakin da jiragen yaki marasa nauyi da ma’aikata da sojoji.

A lokacin da yake bayani a wajen mika jirgin ruwan ga Rundunar Sojin Ruwan kasarsa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan TCG Anadolu ne jirin irin sa na farko a duniya da manyan jiragen yaki masu saukar unglu da marasa matuki za su iya tashi da sauka a kansa.

Ya ce “TCG Anadolu ne jirgin yaki na farko a duniya da manyan jiragen yaki marasa matuka za su iya tashi da sauka a kansa.”

Jirgin ruwa na yaki na TCG Anadolu ne irin sa na farko a duniya/ Photo AA

Jiragen yaki marasa matuka kirar Turkiyya na Bayraktar TB3 da Kizilelma, jiragen sama na yaki samfurin Hurjey za su iya tashi da sauka a kan jirgin na TCG Anadolu, in ji Erdogan.

Jirgin ruwa mai iya kai farmaki daban-daban

Shugaban Turkiyya ya kara da cewa a yanzu Turkiyya za ta iya kai farmaki da gudanar da aiyukan jin kai a dukkan duniya, zai kuma iya daukar manyan motocin yaki masu sulke, madalla da wannan jirgi.

Erdogan ya kara da cewa “TCG Anadolu na da ikon kaddamar da ayyukan soji da na jin kai a dukkan lungu da sako na duniya.”

Dakarun sojin Turkiyya na daga cikin mafiya karfi a duniya/ Phote: AA

Ya ce, jirgin na da fasaha wajen sadarwa da iya bincike da hangen nesa da kula da kai farmakai da sauran su.

Erdogan ya kuma ce kamfanoni 131 ne suka hadu suka yi aikin samar da jirgin ruwan yakin na TCG Anadolu.

Jirgin na da tsayin mita 231 da fadin mita 32, sannan yana da nauyin tan dubu 27,000.

TRT World