Shugaba Erdogan da mai dakinsa Emine Erdogan, tare da rakiyar yara daga yankin kudancin Turkiyya inda girgizar kasa ta shafa, sun tsaya a gabar tekun daga Fadar Dolmabache  don ganin lokacin da jirgin ya tashi daga Zirin Istanbul. (AA)

Jirgin ruwan yakin Turkiyya mafi girma TCG Anadolu ya harba bindiga sau 21 domin nuna girmamawa ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan a yayin da ya tashi daga Tekun Istanbul inda ya nufi Bahar Aswad.

Jirgin ruwan, wanda shi ne irinsa mafi girma a duniya da ba shi da matuki, ya bar gabar tekun Sarayburnu da ke Istanbul inda ya wuce ta Fadar Dolmabahce ranar Lahadi.

A ranar ce aka cika shekara 103 da kafa majalisar dokokin Turkiyya, wadda ake yin bikin kafa ta duk shekara a matsayin ranar Kasa Mai Cin Gashin Kanta da kuma Ranar Yara a Turkiyya.

Shugaba Erdogan da mai dakinsa Emine Erdogan, tare da rakiyar yara daga yankin kudancin Turkiyya inda girgizar kasa ta shafa, sun tsaya a gabar tekun daga Fadar Dolmabache don ganin lokacin da jirgin TCG Anadolu ya tashi daga Zirin Istanbul.

Ministan Tsaro Hulusi Akar da manyan kwamandojin tsaron Turkiyya sun shiga cikin TCG Anadolu, wanda jiragen helikwafta na sojin saman Turkiyya suka yi wa rakiya a yayin da ya wuce ta zirin.

Kamfanin kera jiragen ruwa na Sedef da ke Istanbu ne ya kera jirgin, kuma TCG Anadolu yana iya daukar jirage masu saukar ungulu da jirage marasa matuka da motoci da dakarun tsaro.

Jirage marasa matuka samfurin Bayraktar TB3 na Turkiyya da Kizilelma, da kma jiragen Hurjet da ke kai hari kafin kiftawa-da-bisimilla suna iya sauka da tashi daga jirgib ruwan yakin.

AA