Shugabannin kasashen biyu za su jagoranci taro na biyu na kwamitin hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Aljeriya.Hoto: AA

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya karɓi baƙuncin takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Algiers babban birnin kasar.

Erdogan da Tebboune sun fara ganawarsu a ranar Talata bayan wani bikin maraba da aka yi a fadar shugaban kasar Aljeriya

A yayin ziyarar, shugabannin biyu za su jagoranci taro na biyu na kwamitin hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Aljeriya.

A taron majalisar, za a tattauna matakan ƙara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Erdogan da Tebboune za su kuma yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi yankin da ma duniya baki daya, ciki har da hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza.

AA