Shirin talabijin na TRT World mai suna "Off The Grid," mai kunshe da labari a kan "Ukraine Wartime Diaries," wato "Yadda yakin Ukraine ke gudana", ya lashe Gasar Fim ta Kasa da Kasa ta Emmy a fannin "Labarai da Al'amuran yau da kullum".
Hukumar horarwa kan aikin talabijin da kimiyya ta Amurka NATAS ce ta sanar da wadanda suka yi nasara a fannin labaran a Gasar Emmy karo ta 44 a ranar Laraba a Dandalin Palladium Times da ke birnin New York.
TRT World, wacce ta wakilci kasar Turkiyya a matakin karshe na gasar, ta fafata ne da wasu tasoshin na Burtaniya da Brazil da kuma Isra'ila.
Mouhssine Ennaimi da Alexandre Pauliat ne suka shirya zangon shirin na talabajin da ya yi duba a kan yakin Ukraine din, inda Hakan Hocaoglu ya tsara hotuna, ta hanyar bayyana mummunan tasirin da yakin Rasha da Ukraine ya yi.
Fim din wanda Fatih Kibar ya tace, sannan Mahmut Sami Cavus ya tsara, ya bayyana yadda rayuwa ta dinga sauyawa fafaren hula a Ukraine bayan janyewar dakarun Rasha daga yankunan da dakarun Ukraine suka mamaye.
'Shirin da ya nuna yakin Ukraine'
"Off The Grid," shiri ne mai dogon zango na kafar watsa labaran TRT World da ya lashe kyaututtuka a fannoni da dama, inda ya yi duba sosai wajen harkokin yau da kullum ta hanyar yin binciken kwaf da kuma salon yadda ya fito da labarai masu jan hankalin jama'a ya watsa wa duniya.
A cikin zangon da aka yi wa take da "Ukraine Wartime Diaries," an nuna abin da ya faru bayan janyewar dakarun Rasha daga Ukraine, na wahalhalun da mutane suka samu kansu a ciki.
Bayan kwace yankunan, sai wuraren da yakin ya shafa suka koma inda ake aikata miyagun laifuka sannan ayyukan laifukan yaki suka karu. Abin da ya faru shi ne na yadda wasu fararen hula suka samu kansu a cikin yanayi na tsare su, sauran kuma suka hadu da miyagun kaddarori yayin da wasu suka tsere don tsira da rayuwarsu.
Shirin "Off The Grid" ya yi ta bibiyar tawagogin 'yan jarida na gida da na kasashen waje a kokarinsu na ganin an yi wa mutane adalci a wasu al'amura da ke faruwa a kasashe irin su Bosnia da Lebanon da Kenya da kuma Ukraine.
Gasar tana karrama kwararru ne da suke aiki a manyan matakan watsa labarai da tsara shirye-shiryen talabajin masu ma'ana, in ji Adam Sharp, Shugaban NATAS.
"Ana karrama 'yan jaridar da suke kawo mana labarai a kan manyan abubuwa da suka shafi zamantakewa da al'adu da kuma siyasa. NATAS na alfahari da murnar nasarar ayyukan da suka lashe kyaututtukan na bana."
Masu shirya gasar sun ce sun ji dadin karbar "ayyuka fiye da 2300 da aka shigar da su gasar", daga kafafen watsa labarai na talabajin a fadin duniya.