Sabon shirin TRT World, na Holy Redemption, ya yi nasarar ci gaba da fayyace ayyukan ta'addanci na Yahudawa ‘yan kama wuri zauna da farmakin da suke ci gaba da kai wa Falasdinawa tun bayan da aka nuna shi a ranar 24 ga watan Agusta.
An watsa shirin a lokaci guda a tasoshi shida na TRT na ƙasa a makon da ya wuce kuma ya lashe kyautar mafi kyawun Documentary a bikin bajekolin shirye-shirye na duniya na Al Jazeera, wanda aka gudanar a Sarajevo daga 13 zuwa 17 ga watan Satumba.
Bikin fina-finai na Documentary na Al Jazeera karo na 7, ɗaya daga cikin mafi daraja da ke hado kan masana'antar tsara shirye-shirye, ya mai da hankali ne kan Falasdinu a wannan shekara.
Bikin mai taken "Adalci?", ya jawo hankalin masu shirya fina-finai da masu rarrabawa, da wakilan gidajen talabijin da kwararrun kafofin watsa labarai daga ko ina cikin duniya.
Holy Redemption, wanda aka fara nuna shi a cikin gida a Sinima din Atlas ta Istanbul a ranar 24 ga watan Agusta, an samun nuna shi a matakin duniya a bikin na Sarajevo.
A matsayin daya daga cikin fitattun fina-finai na bikin, ya lashe Mafi kyawu Documentary da Shiri Mafi Kayatarwa kuma ya sami yabo mai yawa daga masu kallo da kwararru daga ko ina a cikin duniya.
Holy Redemption ya sake waiwaye kan abubuwan tunawa masu ciwo na kisan kiyashin Srebrenica, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana shi a matsayin kisan kare dangi, da kuma fallasa irin kisan gillar da Isra'ila ke yi a Falasdinu.
Nunin fim ɗin a Bosnia, inda har yanzu abubuwan tunawa da Srebrenica suke Tamkar sabbi, ya kafa alaƙar jin zafi da motsa rai tsakanin waɗannan kisan kare dangi guda biyu. Tun a ranar 7 ga Oktoba, lokacin da aka fara kisan kiyashi a Gaza, TRT World ta gabatar da wani shiri Mai nuna duhu da shirun da ake yi karo na biyu a kan wannan ta'asa.
Holy Redemption ya bayyana satar filaye da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna na Isra'ila suke yi ta hanyar tattaunawa da shaidu da kuma masu aikata laifin.
An fara nadar shirin watanni biyu bayan Tawagar Bincike ta TRT World ta kutsa cikin kungiyoyin Isra'ila masu tsatsauran ra'ayi a Yammacin Gabar Kogin Jordan, bayan fara kisan kare dangi a Gaza.
An dauki bayanan yadda ake mamaye yankunan Falasdinawa a hankali bisa samun goyon bayan Isra’ila.
Ta hanyar hotunan da aka samo daga cikin wuraren da aka sani da ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi kamar ta "Hilltop Youth" - wanda kafofin watsa labarai na Isra'ila ke bayyana ta da kamar ISIS din Isra'ila - ta kasance ana horar da mambobinta,, lamarin da aka bankado shi ga duniya a karon farko.
Wadanda suka aikata laifin da Shaidu na yadda ake mamayar sun yi magana a cikin wannan Shiri ta hanyar tattaunawa da masu fafutuka na Isra'ila da tsoffin sojojin Isra'ila da shugabannin masu tsattsauran ra'ayi, da Mambobin majalisar dokokin Isra'ila, inda suka bayyana dabarun Isra'ila na korar Falasdinawa da kuma tsare-tsaren satar filaye.
Shirin ya nuna yadda aka kafa matsugunan Yahudawa ba bisa ka'ida ba da yadda aka lalata gidajen Falasdinawa.
Fitattun hirarraki a cikin shirin sun haɗa da Daniella Weiss, shugabar 'yan kama wuri zauna; da Zvi Sukkot, tsohon mamba na Hilltop Youth kuma dan majalisa na yanzu; da tsohon Firaministan Isra'ila Ehud Olmert; da lauya mai fafutuka Michael Sfard; da Hagit Ofran, shugaban kungiyar Zaman Lafiya Yanzu; da Nadav Weiman, tsohon maharbi a cikin sojojin Isra'ila.
Holy Redemption wanda ya lashe kyauatar shiri mafi kyau zai ci gaba da bayar da labarin Falasdinu.