Telly Awards celebrate excellence in video and television across all screens. Others

TRT World ta lashe Kambin 'SIlver Telly Award' a ɓangaren labarai da sadarwa sakamakon bidiyoyin da ta fitar na tarihin gwagwarmayar Yahudawa masu rajin kafa ƙasar Isra'ila.

Bidiyoyin masu rukunai uku sun yi nazari ga yunƙurin da ƙungiyar 'yan Zionist ta yi a ƙarni na 19 don kafa ƙasar Yahudawa a yankuna irinsu Amurka, Argentina da Uganda.

'The Telly Awards', gasa ce mai muhimmanci da ake shiryawa a Amurka, wadda a bana ta karɓi bidiyo sama da 13,000, inda daga waɗanda suka yi nasarar lashe kambi har da Al Jazeera da Al Arabiya dukka a ɓangaren da TRT World ta yi nasara. An karɓi finafinai daga dukkan duniya da ɗaukacin jihohin Amurka 50.

Ɓangare na farko na bidiyoyin ya fara da bayanin tarihi mai jan hankali: kafin su fara mamayar Falasɗinu, Yahudawan Turai sun duba yiwuwar kafa ƙasar Yahudu a Gabashin Afirka. A 1903, suka ƙirƙiri shiri kan 'Uganda' wanda ya yi yunƙurin ƙirƙirar ƙasar Yahudawa daga cikin ƙasar Kenya a yau.

Sashe na biyu na faya-fayan bidiyon kuma ya yi duba ga bayanai na gaskiya da ke da rikitarwa: Yahudawan Zionist a Turai sun duba yiwuwar kafa ƙasa a Argentina. Sun yi hasashen Moise Ville ya zama nan ne makomarsu kafin daga baya hankalinsu ya koma zuwa ga Falasdinu.

Sashe na ƙarshe ya yi bayani kan wani wajen na daban da Yahudawa suka dinga tantamar ƙirƙirar ƙasar Yahudawa - a tsakiyar Amurka. An bai wa wannan aiki da aka yi niyyar yi a New York sunan 'Jihar Yahudawa ta Ararat".

Waɗannan ɓangarori gaba ɗaya sun yi bayanin nau'ikan gwagwarmayar Yahudawa a duniya kafi su mamayi yankin Falasɗinu mai tarihi.

Kwarewa a fannin bidiyo da talabijin

A shekarar 1979 aka fara bikin bayar da Kambin Telly Awards a bangarorin bidiyon da talabijin.

Da fari suna mayar da hankali ga tallace-tallacen Amurka, yankunan da na tauraron dan adam, daga baya kuma sai kambin ya fadada ga bidiyo mai dauke da bayanai daban-daban d asuka shafi batutuwa da dama.

Ta hanyar bayyana aiki mafi inganci a talabijin da bidiyo domin tantance wa, Telly Awards na jan hankalin ayyuka da dama aga kamfanonin talla, gidajen talabijin da masu dab'i a fadin duniya.

Majalisar alkalai - su sama da 200 da ke jagoranci a masana'antar ne ke alkalancin lashe 'Telly Awards'

TRT World ta lashe kambin ne bayan samar da bidiyo mai inganci da ya shafi al'ummar duniya baki daya kuma ake ta tattaunawa a kansa.

TRT World