Saudiyya ta saukaka wa ‘yan kasar Turkiyya matakai da hanyoyin da ake bi don zuwa kasar mai tsarki don Aikin Hajji ko zama a kasar baki daya.
“Shirin Saukaka Hanyar Zuwa Makka” da Saudiyya ta kaddamar a 2019 a matsayin wani bangare na “Shirin Bakin Bautar Ubangiji” ya isa ga Turkiyya.
Manufar shirin ita ce saukaka wa maniyyata aikin hajji duk wasu abubuwa da ake yi kafin tafiya kasa mai tsarki.
Wannan shiri da aka mika ga Turkiyya ya hada da samun biza da fasfo da gwajin lafiya da sauran al’amuran da suka shafi maniyyata aikin hajji kafin su bar kasarsu.
Shirin ya kuma kunshi hanyoyin daukar jakunkuna da jigilar alhazai zuwa kasa mai tsarki da kuma wajen zama bayan an isa.
Shugaban Hukumar Kula da Al’amuran Addinai ta Turkiyya Ali Erbas ya bayyana farin cikinsa a lokacin kaddamar da wannan shiri a filin tashi da saukar jiragen sama na Istanbul.
Erbas ya ce wannan shiri zai saukaka wa maniyyatan Turkiyya zuwa kasa mai tsarki inda za su kammala mafi yawan abubuwan da ake bukata kafin a tafi Saudiyya kamar irin su daukar bayanan yatsu da tantance fasfo a Istanbul wanda a kan yi su ne bayan an sauka a Makka ko Madina.
Tsari da babu irin sa
A yayin da yake yaba wa Saudiyya, Erbas ya ce “Bayan maniyyatanmu sun bar nan, za su shiga motoci ne su tafi masaukansu na otel ba tare da sun tsaya a filin jiragen saman Makka ko Madina ba.”
Ya kara da cewa “Idan muka kalli wahalhalun da ake sha a baya, kamar tsaiwar tantance fasfo da tsaiwar daukar bayanan yatsu, za mu iya cewa wannan gagarumin shiri ne na musamman.”
Darakta Janar na Hukumar Kula da Fasfuna ta Saudiyya Sulaiman bin Abdulaziz Al Yahya, wanda shi ma ya halarci bikin kaddamar da shirin ya ce babu irin wannan tsari a wani waje a duniya a yau.
Al Yahya ya kara da cewa “A lokacin da maniyyata suka shiga jiragen sama daga nan kasar, za su yi tafiyarsu ne kamar suna cikin jirgin saman da ke ziga-zirga a cikin Saudiyya, ya fi sauki ma sama da hawa jirgi a cikin gida.”
Daya daga cikin maniyyata Hasan Ayer mai shekara 45 da zai tafi kasa mai tsarki aikin hajji ta filin tashi da saukar jiragen saman Istanbul ya bayyana gamsuwarsa da wannan sabon shiri inda ya ce tabbas tsarin zai fi amfanar da tsofaffi sosai.