Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan tare da mai dakinsa Emine Erdogan sun halarci bikin mika musu motar Togg T10X kirar Turkiyya da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Ankara.
Ministan Masana’antu da fasahar Kere-Kere Mustafa Varank tare da wadanda suka hada hannu waje guda don samar da Togg, sun mika sakon taya murna ga Shugaba Erdogan da matarsa Emine Erdogan.
Shugaban na Turkiyya da iyalinsa sun karbi mukullai da takardun motocin Togg T10X guda biyu launin ja da shudiya.
A jawabin da Shugaba Erdogan ya yi a wajen bikin karbar motocin ya bayyana cewa tun a shekarar 2019 suka biya kudin motar ta Togg da ta zama abar alfahari ga Turkiyya. A yau kuma sun karbi motocin nasu don fara hawa.
Shugaba Erdogan ya taya dukkan jama’ar Turkiyya murnar wannan nasara da aka samu na samar da mota mai aki da lantarki dari bisa dari a kasar.
Ya kara da cewa motar ta Togg ta samu nasarar dukkan wasu gwaje-gwajen na’ura da aka yi mata.
Erdogan ya ce “In sha Allah daga yau za mu fara hawa motar Togg a kan titunanmu.”