A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Emine Erdogan ta bayyana ƙaunar da take yi wa wadannan mata, tana jaddada cewa hoɓɓasarsu a bar koyi ce sosai. / Hoto: AA

Matar Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta yabi gudunmawar da mata suke bayarwa a fannin noma, a Ranar Mata Monoma ta Duniya, inda ta bayyana muhimmiyar rawar da suke takawa wajen inganta noma don tabbatar da cewa an bar wa 'yan baya abin da za su yi alfahari da shi.

A wajen taron da aka yi albarkacin ranar, mai taken "Matan da Suke Barin Abin Koyi Kan Aikace-Aikacensu", wanda Ma'aikatar Noma ta shirya, Uwargidan Erdogan ta bayyana muhimmancin alaƙar da ke tsakanin mata da inganta noma, tana mai cewa ƙoƙarin kowace mace tamkar dasa "wani tsiro ne na soyayya a zuciyar ƙasa."

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Emine Erdogan ta bayyana ƙaunar da take yi wa wadannan mata, tana jaddada cewa hoɓɓasarsu a bar koyi ce sosai.

A cikin saƙon nata, ta hada da wani bidiyo da ke nuna labaran mata manoma daga ƙungiyoyi daban-daban a faɗin Turkiyya, inda suke ba da labaransu da irin ayyukansu.

Ƙarfafa wa mata gwiwa

Wata manomiya Merve Cakin daga Bursa, ta nuna godiyarta ga Matar Shugaban Ƙasa kan ƙara wa ƙungiyoyin manoman ƙwarin gwiwa.

Cakin ta ƙarfafi mata da su ci gaba da ƙoƙarin cim ma burikansu da fafutukarsu don tabbatar da cewa sun kai ga ci.

Wata manomiyar mai suna Sibel Merveoglu daga Mugla, ta bayyana yadda ta ji kan samun goyon bayan gwamnati da take yi a ko da yaushe, yayin da Nazmiye Dengel daga Kastamonu suka yi fatan samun girbi mai albarka.

Taron ya jaddada muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen tsara makomar noma ta Turkiyya, tare da nuna farin ciki da irin gudunmawar da suka bayar da kuma juriya.

TRT World