Mai dakin shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar kare martabar kananan yara da ke rayuwa a yankunan da ake fama da yaki, tana mai jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don kare rayuwar yara da haƙƙoƙinsu.
A wani saƙon bidiyo da ta aika zuwa ga Taron Matan Shugabanni karo na 4 da aka gudanar a Kiev, ta yi karin haske kan buƙatun yara ƙanana a yankunan da ake yaƙi irin su Ukraine da Syia da Gaza, tana mai cewa duniya na da alhakin samar da duniyar da ba ta yaƙi da mutuwa ba ga yara kanana.
Da take jawabi ga taron, wanda ya mayar da hankali kan "tsaron yara kanana", Erdogan ta bayyana damuwa game da ƙaruwar barazana ga haƙƙoƙin yara a yankunan da ke fama da rikice-rikice.
Ta yi nuni da cewa babban abin bakin ciki na faruwa inda ake binne yara kanana ba tare da tantance su waye ba, kuma ana ganin mutuwar yaran a matsayin asarar yaki kawai.
"Makomar dan adam ta ta'allaka ne ga yara kanana, amma a yau muna shaida yadda duniya ta ki kare hakkokinsu na rayuwa," in ji ta.
Emine Erdogan ta ja hankali na musamman ga matsalar da mutane suke ciki a Gaza, inda yara kanana suke mutuwa a kowanne mintuna goma, kuma tara daga cikin duk yara goma ke fuskantar yunwa da kishirwa. Ta yi tambayar "Ta yaya za mu amince da duniyar da yara ke cewa 'Na gaji sosai', ina son na mutu don na huta, suna zabar mutuwa sama da rayuwa?
Goyon bayan Turkiyya ga yara kanana
Emine Erdoganta kuma ta yi ƙarin haske kan rawar da Turkiyya ke taka wa wajen goyon bayan yara ƙanana da rikici ya raba da matsugunansu, musamman wajen ɗaukar nauyin kula da yara 1,500 na Ukraine.
Ta yaba da kokarin mai dakin shugaban Ukraine Olena Zelensky wajen kare yaran Ukraine, inda ta yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin da 'zaman lafiya mai dore wa".
A shekarar 2021 ne Zelensky ta kirkiri Taron Matan Shugabannin Kasashe, wanda ke da manufar samar da wata inuwa ta kasa da kasa da za ta magance kalubalen da mutane ke fuskanta a duniya tare da gudanar da ayyukan hadin gwiwar don ingantar rayuwar jama'ar duniya.