Mai Ɗakin shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta gabatar da tsohuwar al'adar Turkawa ta haɗa kayan aure ga 'yan kasashen duniya da suka taru a birnin New York a yayin ziyarar da ta kai saboda Babban Taron MDD karo na 79.
Erdogan ta karbi bakuncin wani taro mai taken "Kadarorin Amare: Kayan Aure na Daular Usmaniyya da al'ummar Anatolia," da aka gudanar a Gidan Turkiyya a ranar Talata, inda aka nuna irin muhimmancin da al'adar hada kayan aure ta Turkawa ke da shi, al'adar da aka gada kaka da kakanni.
"Kayan aure na sadaki ba kayan amfanin yau da kullum ba ne kawai, sun hada da kalamai na musamman da suke bayyana jin dadi, fatan alheri da burin 'ya'ya mata," in ji ta.
Erdogan ta yi bayani da cewa wannan al'ada ta haɗa kayan aure ba wai iyakacin shiri ne na amarya don zuwa sabon gida ba - wani kokarin jama'a ne na shigar da dangi da 'yan uwa cikin harkokin wauren wanda ke nufin zaman lafiya da haɗin kai da ƙaunar juna.
Kowane mataki, tun daga samar da kayan aure da kai su gidan amarya, na bayyana daɗaɗɗiyar al'adar jama'ar Anatolia.
"A cikin tarihi baki daya, mutanen yankin sun dinga amfani da kowanne ɓangaren rayuwa suna mayar da shi nasu, suna inganta muhallansu da kayan da suke samarwa."
Kar a cakuda kayan auren Turkawa da tsarin da ake yi a wasu yankunan Kudancin Asiya inda ake tirsasa wa iyayen amarya su karɓi tsabar kuɗi a tsawon wani lokaci a matsayin kuɗin aurenta.
Shirin ya ja hankalin manyan mutane da suka je New York, ciki har da mata da mazajen shugabannin kasashe irin su ta Nijeriya Oluremi Tinubu da prindon Sadriu daga Kosovo, da na Mauritius, da Fiji, da Guatemala da Bosnia da Herzegovina.
Su ma matan shugabannin Girka da Mareva Grabowski-Mitsotakis da na Albania, Linda Rama, tare da Philile Diamini ta kasar Estwatini na daga waɗanda suka halarta