Kashin farko na Turkawa da aka kwaso daga Khartoum, babban birnin Sudan sun isa Istanbul, kamar yadda wani bidiyo da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna.
Kamfanin jirgin saman Turkish Airlines ya kwaso Turkawa kusan 189 daga Addis Ababa, babban birnin Ethiopia bayan sun isa can daga a motoci.
Ranar Laraba ana sa rai karin jiragen sama za su kwaso Turkawa da suka isa Ethiopia daga Sudan.
"Wannan tafiya ce mai matukar wahala. A halin da ake ciki babu wanda ya isa ya fita daga [Sudan] ba tare da taimakon gwamnati ba," a cewar Huseyin Eser, wani Baturke da aka dawo da shi gida.
"[Halin da ake ciki a Sudan] yana da matukar wahala. Ba na sa rai za a kawo karshen rikicin nan kusa. Lamarin ya dagule, muna addu’a ga[Sudan]," a cewar Eyup Kazim Yak, wani Barurke da aka fitar daga Sudan.
Majiyoyin difilomasiyya sun ce an yi amfani da motocin bas wajen kwashe Turkawa 1,600 daga Sudan zuwa Ethiopia.
An ci gaba da gwabza fada ranar Talata tsakanin sojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces [RSF] duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta awa 72 da suka kulla sakamakon shiga tsakanin Amurka da Majalisar Dinkin Duniya.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun ce akalla mutum 459 sun mutu yayin da fiye da 4,000 suka jikkata sanadin rikicin.