Gidan rediyo da talabijin na kasar Turkiyya TRT ya shirya wani taron Ramadan na musamman ga Falasdinu da kuma irin gwagwarmayar da al'ummar Falasdinu ke fuskanta a cikin hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai musu.
A yayin taron "Daren Falasdinu a watan Ramadan" da aka gudanar a ofishin TRT Ulus da ke Istanbul a ranar Juma'a, babban daraktan TRT Mehmet Zahid Sobaci, ya bayyana irin takaicin da yake ji dangane da yaƙin da Isra'ila ke yi a kan Falasɗinawa.
Ya ce, ko ba daɗe ko ba jima, Isra'ila za ta gane cewa ba za ta ɗore tana zubar da jinin yaran da ba su ji ba ba su gani ba.
Sobaci ya ce "Yayin da muke azumin watan Ramadan, zukatanmu na cikin bakin ciki ga halin da 'yan'uwanmu Falasdinu ke ciki na tsananin wahala."
"A yau, muna goyon bayan wadanda ke Gaza da Rafah, da Yammacin Kogin Jordan, muna jaddada cewa ba su kadai ba ne a gwagwarmayar da suke yi."
Sobaci ya kuma soki labaran son zuciya da kafafen yada labarai na Yammacin Duniya ke yadawa. “Duk da gurbatattun bayanan da kafafen yada labarai na Yamma ke yi, mun tsaya tsayin daka wajen bayyana cikakkiyar gaskiya.
Yunkurin da Isra'ila ke yi na ɓoye ayyukanta ba zai iya ɓoye irin ta'asar da ke faruwa a idon duniya ba. Kisan gillar da suke neman boyewa ya bayyana a fili."
Ya ƙara da cewa, "Wannan halin da ake ciki yana nuna rashin tarbiyya da ɗa'a a tsakanin al'ummomin Yammacin Duniya, wadanda ke da'awar kiyaye dabi'un bil'adama na duniya amma galibi suna kasawa a aikace."
"Mun shaida yadda ake amfani da manufar 'yancin fadin albarkacin baki a wasu lokuta a Yammacin Duniya. 'Yancin fadin gaskiya ya wuce iyakokin al'adu kuma ya kamata a yi nasara a duniya," in ji Sobaci.
'Barnar da Isra'ila ta yi a Gaza ta wuce kashi 70 cikin 100'
Da yake jawabi a wajen taron da TRT ta shirya, jakadan Falasdinu a Turkiyya, Dr. Faed Mustafa, ya nanata taken shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ke cewa "Duniya ta fi biyar girma" ya kuma ce, "Tsarin kasa da kasa da ake gudanarwa a halin yanzu bai ceci Falasdinawa ba kuma bai cimma adalci ba. "
Jakadan ya ƙara da cewa "Wannan zaluncin zai kawo ƙarshe ne a lokacin da Falasdinawa za su iya samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu tare da Kudus a matsayin babban birninta."
"Muna magana ne game da lalata fiye da kashi 70 cikin 100 na ƙasar Gaza. Barnar ta shafi komai a Gaza, ciki har da asibitoci da jami'o'i da makarantu da masallatai da kuma majami'u.
Ba su bar komai ba a Gaza," in ji Mustafa. "Gaskiya mu Falasdinawa muna fuskantar mawuyacin hali tsawon watanni shida.
Duk da haka, zaluncin nan ba a ranar 7 ga Oktoba ya fara ba.” A yayin taron, an nuna fina-finai guda biyar, masu dauke da taken "Digital Occupation," da "Zionism: Manufacturing A State," da "Rafah: An Un Safe Haven," da "The Sole Survivor," da kuma "Witness."
Bugu da ƙari, an kuma nuna tallar sauran fina-finan da ke tafe. Fina-finan sun ba da haske kan bangarori daban-daban na rikicin Isra'ila da Falasdinu.