An soma ƙera jirgin tun a shekarar 2016 amma, inda aka kammala a 2023. / Hoto: AA

KAAN, wanda jirgin yaƙi ne da aka ƙera a Turkiyya, an yi gwajinsa a karon farko, kamar yadda hukumar da ke kula da sararin samaniya ta Turkiyya ta tabbatar a ranar Laraba.

Jirgin yaƙin na zamani an ƙera shi ne a cikin ƙasar inda ake sa ran zai shiga cikin jerin jiragen yaƙin Turkiyya.

Wannan ci gaban da aka samu ya sa Turkiyya ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da irin wannan fasahar.

Ƙera jirgin wanda aka soma tun a 2016, an kammala shi a Maris ɗin 2023.

Jirgin mai tsayin mita 21 zai iya kaiwa matsakaicin gudun Mach 1.8, godiya ga tagwayen injinansa, wadanda kowanensu ke iya samar da ƙarfin kilo 13,000 idan jirgin na tafiya.

KAAN yana da sabbin abubuwa na zamani waɗanda suka haɗa da sanar da halin da ake ciki a gaggauce, gano matsala a lokacin yaƙi da sabuwar fasahar yaƙi da kai hari daidai inda ya nufa da kuma wurin ajiyar makamai.

Turkiyya na haɓaka a fannin tsaro

Turkiyya ta zama ƙasar da ke fitar da kayayyakin tsaro, godiya ga irin sauyin da aka samu sakamakon gwamnatin ta Turkiyya ta yanke shawarar samar da makamanta tun farkon shekarun 2000.

Tun daga lokacin, kamfanonin Turkiyya suka rinƙa samar da kayayyakin soji da suka haɗa da bindigogi da motoci masu sulke da makamai masu linzami da jirage maras matuka na zamani waɗanda suka shahara a duniya.

Sashen tsaro na Turkiyya ya bayar da muhimmiyar gudunmawa ga tattalin arziƙin ƙasar inda ya samar da dala biliyan 5.5 a kayayyakin da yake fitarwa, wanda adadi ne da ba a taɓa samu ba a tarihi, wanda hakan ke nufin an samu ƙarin kaso 27 cikin 100 daga shekarar da ta gabata.

Matsakaicin kayayyakin tsaro da ƙasar ke fitarwa ya haura dala 65 a duk kilo ɗaya. Wannan haɓakar ta kasance wata alama ta amincewa da kayayyakin tsaro na Turkiyya, inda adadin ƙasashen da ke karɓar kayan Turkiyya suka ƙaru daga 176 zuwa 185.

TRT World