A ranar 14 ga Agustan 2001 aka kafa Jam'iyyar AKP karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan. A 2003 aka zabi Erdogan a matsayin Firaminista kuma tun 2014 yake matsayin Shugaban Kasa. / Hoto: AA Archive

Jam'iyyar Adalci da Cigaba ta Turkiyya na gudanar da bikin cika shekaru 23 da kafuwa, tsawon lokaci da aka samu zaman lafiya, cigaba da nasarorin zabe.

A ranar 14 ga Agustan 2001 aka kafa Jam'iyyar AKP karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan. A 2003 aka zabi Erdogan a matsayin Firaminista kuma tun 2014 yake matsayin Shugaban Kasa.

A ranar 3 ga Nuwamban 2002, jam’iyyar ta samu gagarumar nasara, inda ta lashe kasha biyu cikin uku na kujerun majalisar dokoki – nasarar da ba a taba gani ba a kasar cikin shekaru da dama.

Jam’iyyar AKP a shiga manyan zabuka bakwai – a 2002, 2007, 2011, 2015, sabon zabe a 2015, Yunin 2018 da a Mayun 2023 a baya-bayan nan.

Tun bayan kafa jam’iyyar a 2001, a karkashin jagorancin Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Turkiyya ta zama mai taka babbar rawa a fagen kasa da kasa, tana daukar matakai daban-daban na kandagarki wajen tunkarar batutuwan kasa da kasa da yankuninta.

A tsawon wadannan shekaru, Turkiyya ta karfafa dangantakarta da kasashen Turai, Turkawa da kasashen Musulmi, tana jagorancin taka rawa a harkokin yankinta.

Ta wannan salo, Turkiyya ta fara bayar da gudunmowa wajen wareware matsalolin duniya da taka rawa a kungiyoyin kasa da kasa.

Ga wasu daga nasarorin Jam’iyyar AK a cikin shekaru 23:

A karkashin yunkurinta na shiga Tarayyar Turai, Turkiyya ta taka yi manyan ayyuka da cimma babbar nasara na zama mambar Tarayyar Turai, ta samar da muhimman sauye-sauye a fannin siyasa da tattalin arziki. A 2005 aka fara tattaunawar shiga Tarayyar a hukumance, wanda lokacin ya zama babbar nasara a tarihin alakar Turkiyya da Tarayyar.

A bangaren shiga tsakani a Gabas ta Tsakiya, Turkiyya ta taka muhimmiyar rawa wajen warware rikice-rikicen yankin, tana shirya tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Siriya a 2008 da ma tsakanin bangarori daban-daban a Labanan.

Turkiyya ta kuma yi kokarin rage rikici da kasashe makota ta hanyar manufarta ta “Manufar Rashin Rikici da Makota”, wadda ke da manufar warware dadaddun rikice-rikice da karfafa kawancen yankin.

A fannin tattalin arziki, Turkiyya ta fadada alakarta ta kasa da kasa, musamman da kasashen Afirka, Asiya da Latin Amurka, tana mai mayar da hankali kan alakar cude ni in cude ka, ta hanyar samar da sabbin damarmakin kasuwanci da Afirka wanda ke kara karfin Turkiyya a duniya.

Dadin dadawa, Turkiyya ta haura manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki da suke samar da kayan taimako idan aka yi duba ga kudaden da kasashen ke samu, ta karbi bakuncin ‘yan kasar Siriya da yaki ya yayyaga, kuma tana shiga ayyukan taimakon jinkai na kasa da kasa.

A karkashin Jam’iyyar AK, Turkiyya samu matsayin shugaba a yankinta a fannin samar da makamashi, ta zama matattarar makamashi tsakanin Gabas da Yamma, inda aka yi manyan ayyuka irin su shimfida bututun Baku-Tbilisi-Ceyhan da bututun TANAP da ya ratsa ta tekun Atlantika.

Kasar ta kuma karfafa alaka da Gabas ta Tsakiya da Afirka, ta kafa kanta a matsayin mai fada a ji a yankunan ta hanyar kasuwanci, diflomasiyya da musayar al’adu.

Duk da samun ‘yar hayaniya a wasu lokutan, Turkiyya ta dabbaka da daidaita alakarta da Rasha, sun hada kai wajen samar da makamashi kamar shimfida bututun TurkStream da kawo karshen yake-yake irin na Siriya.

Matakin wuri da Turkiyya ke dauke wajen ayyukan jinkai a duniya, kamar bayar d ataimako ga Musulman Rhingya na Myammar da kasashen Afirka, tare da goyon bayan manufofin Falasdinawa ya daukaka kimar kasar da mayar da ita jagora a duniya wajen bayar da taimakon jinkai.

A 2022, Turkiyya ta shige gaba wajen ganin an kulla yarjejeniyar jigilar hatsi ta tekun Bahar Maliya, wadda ta bayar da damar jigilar hatsi daga tashar jiragen ruwanUkraine a lokacin da ake tsaka da yaki a kasar.

Wannan ya sake bayyana Turkiyya a matsayin babbar mai shiga tsakani a rikice-rikicen duniya. Wadannan nasarori na kasashen waje sun bayar da gudunmawa wajen habakar Turkiyya da girmamar karfin fada a jinta a duniya a karkashin Jam’iyyar AK ta Erdogan.

Nasarorin tattalin arziki

Kafin Jam’iyyar AK, tattalin arzikin Turkiyya na fama da matsaloli da dama, irin su tashin farashin kayayaki mara misaltuwa, kudin ruwa da yake gagarar jama’a biya, da rashin aikin yi da yawa tare da rikicin siyasa.

Bayan shiga ofis a karshen 2002, Jam’iyyar AK ta mayar da hankali wajen tabbatar da habakar tattalin arziki da lafiyar tsarin ta’ammali da kudade.

Gwamnatoci karkashin shugabancin Erdogan sun dinga tabbatar da an yi aiki da dokoki ne, musamman a bangaren ayyukan banki da sha’anin kudi.

Tare da tabbatar da gaskiya a sha’anin juya kudade da kokarin inganta kasuwanci, shekarun farko na Jam’iyyar AK sun shaida daukar muhimman matakai, irin su rage sifiri shida daga kudin kasar a 2005 da sakko da tashin farashin kayayyaki zuwa lamba daya.

Wadannan matakai sun daga darajar Lira din Turkiyya a kasuwar duniya. Hakazlaika, ya zuwa 2013, Turkiyya ta kammala biyan dukkan basukan da IMF ke bin kasar na dala biliyan 23.5.

A farkon shekarun 2000, an samu habakar tattalin arzikin Turkiyya. A tsakanin 2000 da 2007, tattalin arzikin kasar ya habaka da kasha 7.2.

Wannan habaka ta sanya Turkiyya zama daya daga cikin manyan kasuwanni a duniya. Kasar ta kuma tsira daga rikicin tattalin arzikin duniya na 2008 da kankanuwar asara.

Tun zuwa Jam’iyyar AK mulki a 2002, kudin da Turkiyya ke samu a cikin gida ya karu daga dala biliyan $415 zuwa ga sama da dala tiriliyan $1 a 2024.

A gefe guda kuma, kudin da kowanne dan kasa ke samu a shekara ya ninka a wannan wa’adi.

Nasarori a fannin masana’antar tsaro

Turkiyya ta dauki matakai masu muhimmanci kuma ta samu manyan nasarori a masana’antar tsaro.

Ayyukan da aka yi da nasarorin da aka samu a wannan lokaci sun mayar da Turkiyya ta zama mai karfi a yankinta d arage dogaron da take yi a kan kasashen waje.

A tsawon mulkin Jam’iyyar AK, zuba jari a masnaa’antar tsaron Turkiyya ya karu sosai. A yayinda a 2002 aka yi kasafin dala biliyan $5.5, a 2023 adadin ya kai dala biliyan $75.

Kasashin kudin bincike da habaka kayayyaki da ilimi ya karu, hakan ya bayar da damar cigaban fasahar kere-kere a wannan fanni. An inganta samar da kayayyakin a cikin gida, an kuma samar da sabbin fasaha.

Kazalika, an samar da cigaba sosai wajen habaka tsarin tsaro na kasa kuma na cikin gida a zamanin mulkin AKP. A karkashin haka, an fara aikin TF-X, jirgin sama na farko kirar Turkiyya, da samar da jirgin yaki na farko marar matuki a Turkiyya.

Wadannan jirage na UAV da AUAV, tare da Bayraktar TB2 da Anka sun bayar da gudunowa a yaki da ta’addanci musamman yakar OKK/YPGda rassanta, ana kuma habakakarfin samar da kayan tsaro a Turkiyya.

Haka kuma, gwamnatin Jam’iyyar AK ta kaddamar da jirgin ruwanta mafi girma domin amfanin dakarunta na ruwa.

A wani bangare na aikin MILGEM, jirgin ruwa na kasa, a 2011 an kaddamar da amfani da jirgin yaki na Turkiyya d ata kera da kanta na farko, TCG Heybeliada (F-511). An samu ci gaba sosai a fannin sufurin teku, tare da samar da jiragen ruwa na cikin gida da dama ciki har da masu yawo a karkashin teku.

An kuma samu dimbin nasarori a fannin samar da makaman roka da makamai masu linzami a karkashin mulkin Jam’iyyar AK. Makamai masu linzami na cikin gida, irin su SOM, ATMACA, sun shiga jerin kayan tsaro da dakarun Turkiyya suka samar.

Kazalika, an kammala samarwa da fara aiki da garkuwar makamai masu linzami kirar Turkyya, Hisar-A da Hisar-O. A lokacin mulkin Jam’iyyar AK, fitar d akayan tsaro daga Turkiyya ya karu sosai.

Daga dala miliyan $248 a 2002 zuwa dala biliyan $4.4 a 2023. Wannan nasara ta sanya Turkiyya zama mai taka muhimmiyar rawa a masana’antar tsaro a duniya.

Jam'iyyar AK Party ta karfafa mulkin dimokuradiyya

Jam'iyyar AK a ƙarƙashin Recep Tayyip Erdogan ta ƙaddamar da manyan sauye-sauye na siyasa don ƙara tabbatar da mulkin dimokraɗiyyar ƙasar Turkiyya da cibiyoyinta, da nufin shigar da ita cikin ƙungiyar EU.

Amma a shekara ta 2007, lokacin da aka shirya zaɓen shugaban ƙasar a majalisar dokoki, rikicin siyasa ya kunno kai. Sojoji sun fitar da sanarwa ta imel kan gwamnatin da Erdogan ke jagoranta, inda suka bayyana rashin amincewarsu da ɗan takarar Jam'iyyar AK Party, Abdullah Gul, wanda matarsa ke sanya hijabi.

Takardar ta e-mail din ta zo ne a matsayin martani ga muhawarar da wasu ‘yan siyasa da masu sharhi suka yi, inda suka kare wata tsantsar fassarar da aka yi wa lauyoyin Faransa, suna masu cewa zaben shugaban kasar da matarsa ke sa hijabi zai gurgunta tushen tsarin mulkin kasar Turkiyya.

Ba kamar tsoma bakin da aka yi a baya ba, gwamnatin Erdogan ba ta shiga cikin matsin lambar sojoji ba, ta kuma yi kira da a gudanar da zaben raba gardama a watan Oktoba domin sauya kundin tsarin mulkin kasar don kafa dokar zaben shugaban kasa ta hanyar kuri'ar jin ra’ayin jama'a.

Jam'iyyar AK Party ta samu gagarumar nasara a zaben raba gardama da aka gudanar a watan Oktoba inda kashi 69 cikin 100 suka kada kuri'ar 'amincewa', inda suka zabi zababbun shugabannin da kuri'ar al'ummar kasar mafi yawa.

Da dama dai na ganin hakan ya kawo wargaza tasirin da sojoji ke da shi a siyasar Turkiyya, domin kuwa Jam'iyyar AK Party ita ma ta samu gagarumin rinjaye a zaben da aka yi a watan Yuli kafin zaben raba gardama. Bayan wannan sauyi, sojoji sun ci gaba da yin ƙasa a gwiwa a kan shugabancin farar hula.

A cikin 2013, gwamnatin AK Party ta kuma soke sashe na 35 na dokar aikin soja na cikin gida, wanda ya bai wa sojoji damar shiga cikin harkokin siyasar farar hula. A shekarar da ta zo bayan nan, an zabi Erdogan a matsayin shugaban kasar a karon farko ta hanyar samun mafi yawan kuri'ar jama'a.

Amma kuma, a ranar 15 ga Yuli, 2016, wasu ɓata-gari a cikin sojojin Turkiyya suka kaddamar da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba. Wadannan 'yan kungiyar ta'adda ta FETO da ke da nufin kutsawa cikin cibiyoyin gwamnati, sun yi wani mummunan yunkuri na hambarar da Erdogan ta hanyar wani mummunan juyin mulki.

Erdogan da abokansa na dimokradiyya sun sake yin nasara a kan masu yunkurin juyin mulkin. A cikin 2017, Erdogan ya sake kira a gudanar da wata ƙuri'ar raba gardama don sauya tsarin majalisar dokokin kasar zuwa tsarin shugaban kasa, da nufin kafa tsarin siyasa mai tsauri kan duk wani tsoma bakin soja.

An amince da matakin, kuma Turkiyya ta zauna a kan tsarin shugaban kasa.

An kawo karshen mulkin juyin mulkin da aka yi a Turkiyya gaba daya, inda aka shafe shekaru 23 ana mulkin dimokradiyya ba tare da tsangwama ba. A cikin wannan lokaci, jam'iyyar AK Party ta zama jagora a dukkan zabuka shida da ta shiga, wanda ya kara tabbatar da dimokuradiyya a Turkiyya.

TRT World