Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'adda biyar a gabashin ƙasar, ciki har da wanda aka daɗe ana nema ruwa-a-jallo.
"An kawar da 'yan ta'adda biyar a yankin karkara na gundumar Dogubayazit da ke lardin Agri da kuma ƙauyen Palamut na gundumar Hasankeyf da ke lardin Batman, a wani samame da aka yi wa laƙabi 'BOZDOGAN-43'," in ji Ministan Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Alhamis.
A cikin 'yan ta'addan da aka kawar har da Yilmaz Oner, wanda ke da inkiya Sehmus Malazgirt, wanda kuma kuma ke cikin waɗanda Ma'aikatar take nema ruwa-a-jallo.
A cewar Yerlikaya, Oner yana da hannu a hare-hare 18 na ta'addanci da suka yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 27 da fararen-hula huɗu, da jikkata jami'an tsaro 68 da fararen-hula biyu.
Bayanan sirri sun tabbatar da cewa Oner ne ya bayar da umarni da kai waɗannan hare-hare, in ji ministan.
Uku daga cikin 'yan ta'addan da aka halaka suna cikin waɗanda ake neman amma ba ruwa-a-jallo ba.
A kusan shekaru 40 da ƙungiyar ta'addanci ta PKK ta kwashe tana kai hare-hare, ta kashe mutum fiye da 40,000, ciki har da mata da yara da jarirai. Ƙasashen Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci.