Jami'an tsaron Turkiyya sun 'kassara' 'yan ta'addar PKK/YPG 14 a Arewacin Siriya

Jami'an tsaron Turkiyya sun 'kassara' 'yan ta'addar PKK/YPG 14 a Arewacin Siriya

Ma'aikatar Tsaro ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka kai hari kan sojojin Turkiyya a yankin Tsaron Firat.
'Yan ta'addar PKK na yawan buya a arewacin Siriya da Iraki tare da shirya kai hari Turkiyya. / Hoto: AA Archive

Jami'an tsaron Turkyya sun kassara 'yan ta'addar PKK/YPG a Arewacin Siriya, in ji Ma'aikatar Tsaro ta Kasar.

Sanarwar da Ma'aikatar ta fitar ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka buɗe wuta kan sojojin Turkiyya a yankin Tsaron Firat.

Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar 'kassarawa' da nufin kashewa ko kamawa ko miƙa wuyan ƴan ta'addar da ake magana a kai.

Turkiyya ta tsaurara ayyukanta na murƙushe ƙungiyoyin ta'addanci a Arewacin Siriya da Iraƙi, bayan wasu sabbin hare-hare da PKK suka kai a ƴan kwanakin nan, inda suka kashe sojojin Turkiyya 21.

'Yan ta'addar PKK na yawan ɓuya a Arewacin Iraƙi da Siriya tare da shirya kai hare-hare cikin iyakokin Turkiyya.

A hare-haren ta'addanci da ta dauki shekara 35 tana kaiwa a Turkiyya, kungiyar PKK da Turkiyya da Amurka da Ingila da Tarayyar Turai suka bayyana a matsayin ta ta'addanci, ta yi ajalin sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da jarirai.

TRT World