Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta "kawar" da wani babban dan ta'adda na kungiyar PKK a yankin arewacin kasar Iraki da ke kan iyaka da Turkiyya, a cewar wata sanarwa da majiyoyin tsaro suka fitar.
An kawar da dan ta'addan mai suna Celal Birdal wanda ake yi wa lakabi da Sidar Serhat a wani samame da aka kai a yankin Gara, a cewar majiyoyin a ranar Laraba.
Birdal, wanda daya ne daga cikin jami’an da ke tattaro bayanai da kuma adana su ga kungiyar PKK, ya dade yana aiki a cikin kungiyar tun lokacin da yake karatun injiniya a jami'a.
Dan ta'addan shi ya jagoranci wasu 'ya'yan kungiyar zuwa Turkiyya domin kai hare-haren ta'addanci, kuma shi ke kan gaba wajen kai hare-hare da dama kan jami'an tsaro a yankunan Zap da Hakurk da ke arewacin Iraki.
Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar ''kawarwa'' ga 'yan ta'addan da suka mika wuya ko aka kashe su ko aka kama su.
Yan' ta'adda na PKK sukan fake ne a kan iyakar arewacin Iraki, don shirya kai hare-hare.
A tsawon shekara sama da 35 da kungiyar ta yi tana ta'addanci a Turkiyya - kasar Turkiyya da Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ta'addanci wacce ke da alhakin mutuwar mutum kusan 40,000 da suka hada da mata da yara har da jarirai.