Jami'an tsaron Turkiyya sun kama mai kula da harkokin kuɗi na Hukumar leƙen Asirin Isra'ila Mossad, bayan wani bincike da Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) suka gudanar.
Mahukunta sun bayyana cewa Liridon Rexhebi, da ke aiki karkashin umarnin hukumar leƙen asiri ta Isra'ila, ya gudanar da bincike da bin diddigi da jirgin drone, tare da shiirya kai hari kan 'ya siyasar Falasdinawa.
Ya kuma tura kudade ga masu yi musu hidima a Turkiyya, wadanda suke tattara bayanai a Siriya.
Jami'an leƙen asiri na Turkiyya sun bi sahun Lirido Rexhepi bayan ya shigo Turkiyya a ranar 25 ga Agusta, inda ta bincike rawar da yake takawa wajen daukar nauyin ayyukan Mossad a Siriya da kuma kai hari da farmaki kan Falasdinawa.
Sakamakon kokarin da aka yi tsakanin Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) da Sashen Yaki da Ta'addanci na helkwatar 'Yan sandan Istanbul, an kama Rexhepi a ranar 30 ga Agusta.
Majiyoyin tsaro sun bayar da rahoton cewa a lokacin tuhumar farko da aka yi masa, Rexhepi ya yi ikirarin aika kudade zuwa Turkiyya, inda daga baya kotu ta tsare shi tare da gurfanar da shi.
Mossad na aiko da kudaden aikinta zuwa Turkiyya daga kasashen Kosovo da wasu kasashen gabashin Turai.
Bayan bin diddigin aiko da kudaden, an bayyana cewa an aika kudaden da aka karba a Turkiyya daga Kosovo zuwa kaar Siriya ta hanyar Western Union da kudin kiripto.