"An ƙididdige wannan adadi a matsayin mafi yawan fasinjojin da aka taɓa samu tun bayan bude filin jirgin saman Istanbul," in ji Uraloglu. / Hoto: AA Archive

Filin jirgin saman Istanbul ya kafa tarihi a ranar 30 ga watan Yuni inda ya karɓi mafi yawan fasinjoji a fiye da kowane lokaci, in ji Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya.

Ministan Sufurin Abdulkadir Uraloglu ya ce "Filin jirgin saman Istanbul na kafa wani sabon tarihi a kowace rana a matsayin shaida kan muhimmancinsa a duniya a matsayinsa na cibiyar zirga-zirgar jiragen sama mafi muhimmanci a duniya, kuma muna alfahari da ƙaruwar nasarorin da ya samu."

Filin jirgin saman Istanbul ya karɓi fasinjoji 268,275 a ranar Lahadin da ta gabata, wanda hakan ya karya tarihin bara na yawan matafiya da aka samu a rana guda, in ji Uraloglu a ranar Litinin.

Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa, fasinjoji 205,721 ne suka sauka a filin jirgin ta jiragen ƙasashen duniya da kuma wasu 62,554 na jiragen cikin gida a ranar 30 ga watan Yuni, ranar karshe ta wata.

"An ƙididdige wannan adadi a matsayin mafi yawan fasinjojin da aka taɓa samu tun bayan bude filin jirgin saman Istanbul," in ji Uraloglu.

Ministan ya ba da rahoton cewa, jimillar zirga-zirgar jiragen sama a ranar Lahadin da ta gabata ya kai 1,592, inda jirage 1,214 suka sauka daga ƙasashen waje sai kuma 378 na cikin gida.

Uraloglu ya ce kafin wannan lokaci, an kafa tarihin fasinjoji mafi yawa da filin jirgin ya taɓa karba ne a ranar 2 ga Yuli, 2023 da suka kai 265,961.

An karɓi baƙuncin mutum miliyan 82

Ministan Sufuri da ababen more rayuwa na kasar ya bayyana cewa, filayen jiragen saman Turkiyya sun karɓi baƙuncin fasinjoji miliyan 82 a cikin watanni biyar da suka gabata.

Adadin fasinjojin ya karu da kashi 12.7 bisa 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, in ji Abdulkadir Uraloglu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake ambato bayanan hukumar kula da filayen jiragen sama ta jihar (DHMI).

Kimanin fasinjoji miliyan 37.1 ne suka yi zirga-zirgar da jiragen cikin gida, wanda ya karu da kashi 11.1 cikin 100 a duk shekara, kuma fasinjoji miliyan 44.9 sun shiga kasar da jiragen ƙasashen waje, adadin da ya zama kashi 12.7 bisa 100 sama da adadin na bara, a cikin watanni biyar.

Dakon kaya da aka yi ya kai tan miliyan 1.7 a daidai irin wannan lokacin, in ji ministan. Filin jirgin saman Istanbul ya karbi bakuncin fasinjoji miliyan 31 a cikin watanni biyar, wanda ya karu da kashi 8 bisa dari a duk shekara, da jirage 207,800, wanda ya zama kashi 5 cikin dari fiye da adadin bara.

Filin tashi da saukar jiragen sama na Sabiha Gokcen, na biyu mafi yawan zirga-zirga a Turkiyya da yake yankin Anatoliya na Istanbul, ya karɓi baƙuncin fasinjoji miliyan 16.2 a cikin lokaci guda, wanda kashi 20 cikin 100 ya zama sama da adadin na bara, da jirage 96,700, wanda ya karu da kashi 10 cikin 100 duk shekara.

TRT World