Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa ta shirya ƙaddamar da hare-haren soji a Syria muddin ba a cika sharuɗɗan da ta gindaya kan ƙungiyar ta'addanci ta PKK/YPG ba.
“Idan ba a yi abin da muke buƙata game da ƙungiyar ta'addanci ta PKK/YPG ba, za mu ɗauki matakin da ya dace,” in ji Fidan, yayin da yake tattaunawa da CNN Turk ranar Alhamis da maraice.
“Za a ɗauki matakin soji,” a cewar Fidan.
Ya yi wannan kalami ne a yayin da ake ci gaba da tayar da jijoyin wuya game da kasancewar ƙungiyar YPG a Syria, wadda wani ɓangare ne na PKK, wacce ƙasashen Turkiyya da Amurka da Ƙungiyar Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci.
Wa'adin da aka bai wa YPG
Da aka tambaye shi cewa shin Turkiyya za ta ɗauki matakin soji Syria duk da yiwuwar adawa da hakan daga Amurka, Fidan ya fayyace matsayarTurkiyya ba tare da shayi ba.
“Matsayinmu a bayyane yake. Mun shaida wa Amurka da kuma 'yan jarida. Domin su gaya wa su wa? Su shaida wa YPG,” in ji Fidan.
"Mun yi hakan a baya a Afrin, in Ras al Ayn, da kuma Tal Abyad," yana tuna abubuwan da suka yi a wasu yankuna na arewacin Syria inda Turkiyya ta ƙaddamar da hare-hare kan 'yan ta'adda.
Ya ƙara da cewa Turkiyya ba za ta yi ƙasa-a-gwiwa ba wajen sake kai hare-haren.
"Wannan mataki ne da ake buƙata domin tsaron ƙasarmu. Ba mu da wani zaɓi da ya wuce hakan."
Babban jami'in diflomasiyya na Turkiyya ya buƙaci mutanen da ƙasashen duniya suka ayyana a matsayin 'yan ta'adda waɗanda suka tafi Syria daga Turkiyya, Iran, Iraƙi da kuma manyan shugabannin PKK su fice daga ƙasar.